✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Binuwai

Sojoji sun kwato wata mota da kakin sojoji a hannun masu garkuwa a mutanen.

Rahotanni daga Jihar Binuwai na cewa dakarun Operation Whirl Stroke sun kashe wasu mutum uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a garin Zaki Biyam da ke Karamar Hukumar Ukum ta jihar.

Wadanda ake zargin sun gamu da ajalinsu ne a daidai lokacin da suke kokarin tserewa da mutanen da suka sace a cikin wata karamar mota kirar Toyota Corolla.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na rana a ranar Talata, kamar yadda Mashawarcin Gwamnan Binuwai kan Shana’anin Tsaro, Laftanar Kanar, Paul Hemba (mai murabus), ya shaida wa manema labarai.

Jami’in ya ce, “A ranar 24 ga Mayun 2022 da misalin karfe 3:20 na rana, wani wanda aka fi sani da Ordada tare da tawagarsa suka sace wani mai suna Omemma Chimobi dan kabilar Ibo a garin Zaki Biyam.

“Bayan samun bayani a kan haka ne sai jami’anmu suka bi sawun barayin suka kuma cin musu a daidai lokacin da suke neman hanyar ficewa daga garin.

“Ganin dakarun ke da wuya, sai barayin suka bude wuta  su ma sojoji suka maida martani wanda a karshe aka sheke uku daga cikin barayin.”

Hemba ya kara da cewa, dakarun nasu sun samu nasarar kubutar da Omemma Chimobi daga hannun ’yan ta’addan.

Ya ce bindigogi da karamar mota kirar Toyota daya da kakin soja na daga cikin kayayyakin da aka kwace a hannun masu garkuwar.