✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe ’yan bindiga da dama a Zamfara

’Yan bindiga da dama sun sheka lahira bayan sojoji sun ragargaje su.

Sojoji sun hallaka ’yan bindiga masu tarin yawa a wani dauki-ba-dadi a aka gwabza tsakaninsu a Karamar Hukumar Talata Marafa ta Jihar Zamfara.

’Yan bindigar sun gamu da gamonsu a hannun sojoji ne bayan da suka yi wa dakarun kwanton bauna a hanyar Mayanchi zuwa Dogon Karfe da Fagantama.

Kakakin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Birgediya Onyema Nwachukwu, ya ce, bayan ’yan bindiga sun bude wuta, nan take sojoji suka mayar da martani, suka kuma aika da dama cikinsu lahira.

Nkwachukwu ya ce an kwato bindiga kirar PKT da tarin albarusai a hannun maharan da ragowarsu suka tsere da raunukan harbi.

Sanarwar da ya fitar ta ce a wani harin na daban kuma, sojoji sun kashe ’yan bindiga biyar a Karamar Hukumar Bungudu ta Jihar.

Ya ce an kwato bindiga kirar AK 47 da babur da wayoyin hannu daga ’yan bindigar da suka tarwatse bayan an kashe ’yan uwansu.

Ya bayyana jinjinar Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Manjo-Janar Faruk Yahaya, ga sojojin, “Tare da kira da su kara azama domin murkushe ayyukan ’yan bindiga a fadin Najeriya.

“Ya kuma yi roko ga al’ummar yankin Arewa maso Yamma da su rika taimaka wa sojoji masu yaki da ayyukan ’yan bindiga da bayanai domin  kakkabe ragowar bata-garin.”