✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram 3 Borno 

Sojojin rundunar Operation Hadin Kai da ke yankin Arewa maso Gabas sun kashe ’yan ta’addar Boko Haram uku a wani harin kwantan bauna da suka…

Sojojin rundunar Operation Hadin Kai da ke yankin Arewa maso Gabas sun kashe ’yan ta’addar Boko Haram uku a wani harin kwantan bauna da suka kai.

Wani rahoto ya bayyana cewa sojojin tare da rundunar hadin gwiwa ta Civilian Task Force sun yi wa ’yan ta’addar kwanton bauna ne a yankin Karamar Hukumar Gubio ta Jihar Borno.

Wani jami’in leken asiri, ya shaida wa Zagazola Makama, masani kan yaki da ta’addanci kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi cewa, an yi wa wasu ’yan ta’addan Boko Haram kwanton bauna, wadanda suka addabi al’umma tare da sace dabbobinsu zuwa ga Taunin Mandara a Gwoza.

Majiyar ta ce sojojin sun kashe uku daga cikin ’yan ta’addan na Boko Haram tare da kwato bindigogi kirar AK 47 guda biyu da Babur daya da sauran kayayyaki.