✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 49 a dajin Sambisa

An kai hari ne a yankuna uku na dajin

Akalla yan ta’addan Boko Haram 49 ne suka mutu a lokacin da wasu jiragen yakin sojojin saman Najeriya samfurin ‘Super Tucano guda biyu suka kai harin bom a maboyar yan ta’addan guda uku da ke dajin Sambisa a jihar Borno.

Rahotanni sun nuna rundunar sojin sama ta hannun rundunar Operation Hadin Kai ta kai hare-hare da dama ta sama a ranakun 30 da 31 ga watan Agustan 2022.9.

An kai hare-haren ne a sansanonin ’yan ta’addan Gargash da Minna da Gazuwa, dukansu a karamar hukumar Bama ta jihar ta Borno.

Wani jami’in leken asiri ya shaida wa Zagazola Makama, masanin yaki da ta’addanci a Tafkin Chadi cewa harin da jiragen suka kai kan wata babbar motar ’yan ta’adda a Gargash inda suka kashe dukkan mutanen da ke ciki a ranar 30 ga Agustan 2022.

Majiyar ta kara da cewa, jiragen yakin sun sake kai hari a wani wurin da aka ba da sunan shi da Minna, inda suka halaka mayakan Boko Haram da dama yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga a jikinsu.

Kazalika, a ranar 31 ga watan Agusta, an sake kai wani hari ta sama a Gazuwa bayan binciken sirri da aka gudanar ya nuna cewa akwai dimbin mayakan da ke yin hada-hadar kasuwanci a yankin.

Don haka rundunar ta ATF ta yi cikakken bayani kan jiragen yakinta da suka kai farmaki a wuraren biyu, inda suka kashe ’yan ta’adda da dama tare da lalata kayayyakinsu, inda aka ga wasu daga cikinsu sun kone kurmus.

Majiyoyin sun ce an kashe ’yan ta’adda kusan 29 a Gazuwa, an kashe wata babbar mota dauke da mayaka hudu a Gargash yayin da wasu mayakan 16 suka kwashi kashinsu a hannu a yankin Minna a jihar ta Borno.

Manyan majiyoyin leken asirin sun yi nuni da cewa, rundunar sojin saman Najeriya da ke aiki tare da sojojin kasa, za su ci gaba da kai farmakin da suke kai wa ’yan ta’adda a yankin na Arewa maso Gabas.

Idan za a iya tunawa, a kwanakim baya, Babban Hafsan Sojin Sama, Iya Mashal Oladayo Amao, ya bukaci kwamandojin rundunar da su yi duk abin da za su iya tare da tabbatar da cewa sun yi amfani da karfinsu a kan ’yan ta’adda da ke barazana ga tsaro a kasar nan.