✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 6 a kasuwar ’yan ta’adda

Wani kwarrare a harkar tsaro a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya shaida wa wakilinmu cewa, ana tsaka da hada-hada ne a kasuwar sojojin suka…

Rundunar tsaro ta hadin guiwa sun kashe wasu ’yan Boko Haram shida tare da kama wasu da dama, a wani sumame da suka kai wata haramtacciyar kasuwar ’yan ta’adda a Karamar Hukumar Bama a jihar Borno.

Wani kwarrare a harkar tsaro a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya shaida wa wakilinmu cewa, ana tsaka da hada-hada ne a kasuwar sojojin suka dirar mata a a safiyar Laraba.

Ya ce ganin tawagar tsaron ne ya sa ’yan ta’addan suka bude wuta, sai dai ba su samu  nasarar kashe kowa ba, sai ma mutum shida daga cikinsu da aka kashe.

Tuni dai aka mika su hedikwatar rundunar tsaron da ke Bama domin ci gaba da bincike.

Haramtacciyar kasuwar da ake kira Daula dai, na kauyen Bararam, kuma ana cinikin kayayyaki ne da suka hada da kayan abinci da miyagun kwayoyi da gwanjon sutura da man fetur.

Bincike ya kuma nuna cewa ’yan ta’addan da ke gudanar da ita na bada kayan ne don musaya da karafuna.