✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 8 a Borno

Sojojin sun kuma kwace makamai da babur din 'yan ta'addan

Sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar yan banga sun kashe mayakan Boko Haram takwas tare da kama daya da ransa a wani harin kwanton-bauna da suka kai a Karamar Hukumar Mafa ta Jihar Borno.

Dakarun, wadanda ke karkashin rundunar tsaro ta Operation Hadin Kai sun sami nasarar ce a harin da suka kai a daren Litinin.

Hakan ya biyo bayan ziyarar da Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya Laftanar Janar Farouk Yahaya ya kai, inda ya bukaci sojoji da su kara kaimi wajen fatattakar ’yan ta’adda a dajin Sambisa da yankin Tafkin Chadi.

Rahotanni sun ce nasarar ta biyo bayan tattara bayanan sirri a unguwar Ngoum da ke kusa da Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Dakarun sun fatattaki ’yan ta’addan tare da halaka takwas daga cikinsu nan take kamar yadda majiyarmu ta nuna.

Wani jami’in leken asiri ya shaida wa Zagazola Makama, wani mai sharhi kan harkokin tsaro kuma masani kan yaki da tada kayar baya a Tafkin Chadi cewa, ’yan ta’addan su ne wadanda suka saba yin fashi da makami a fadin kananan hukumomin Mafa da Jere da Konduga a Jihar ta Borno.

“Dakarunmu sun kashe takwas daga cikinsu, sun kama daya a raye, sannan sun kwato babura hudu da bindigogi kirar AK-47,” inji majiyar.

A wani labarin kuma, wata kungiya ta ’yan kabilar Kwayam a Borno da ta shahara wajen yaki ta amfani da wani sihiri, ita ma wasu jarumanta sun yi nasarar kashe wasu mutane biyu da ake zargin ’yan Boko Haram ne.

Suj kashe ’yan ta’addan ne a wani harin kwanton-bauna da suka aiwatar ta hanyar amfani da baka da kibiyoyi.

Majiyoyi sun ce ’yan kabilar sun kuma kwato babur guda daya daga hannun ’yan ta’addan wanda daga baya aka mika su ga sojoji a Gwongulan.