✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram, Sun Ceto Matafiya A Borno

Dakarun rundunar sojin Najeriya ta Operation Hadin Kai sun kashe mayakan Boko Haram 10 a wani harin kwanton bauna da kungiyar ta kai a hanyar…

Dakarun rundunar sojin Najeriya ta Operation Hadin Kai sun kashe mayakan Boko Haram 10 a wani harin kwanton bauna da kungiyar ta kai a hanyar Magumeri zuwa Gubio a Arewacin Jihar Borno.

Bayanai sun nuna dandazon ’yan ta’addan sun kai harin ne a kan babura suka yi awon gaba da wasu kananan motoci biyu da fasinjojin cikinsu a kusa da kauyen Titiya a ranar 12 ga watan Yuli.

Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Yankin Tafkin Chadi ya ambato wata majiyar tsaro na cewa, ganin haka ne sojoji suka kai wa matafiyan dauki, tare da ragargazar ’yan ta’addan, sai da suka cika bujensu da iska.

Majiyar ta ce sojojin sun kashe 10 daga cikin ’yan ta’addan, ragowar kuma suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Rahoton ya ce sojojin sun kubutar da dukkan fasinjojin, tare fa mayar da motocin da aka sace ga masu su.

Zagazola ya ce ’yan Boko Haram sun zafafa ayyukan fashi da makami a kan tituna a ci gaba da ayyukansu na ta’addanci a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.