✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kubutar da mutum 10 a hannun ’yan bindiga

Dakarun sojin Najeriya sun ceto mutm 10 da aka yi garkuwa da su tare da hallaka wani dan bindiga a Jihohin Zamfara da Kastina. Kakakin…

Dakarun sojin Najeriya sun ceto mutm 10 da aka yi garkuwa da su tare da hallaka wani dan bindiga a Jihohin Zamfara da Kastina.

Kakakin Rundunar Tsaro ta Najeriya, Manjo-Janar John Enenche ya ce sojojin da ke sintiri sun ragargaji masu garkuwar a kauyukan Gidan Dan Nunu da Dutsi na Karamar Hukumar Zurmi, Jihar Zamfara.

Ya ce a nan ne dakarun suka yi nasarar kubutar da mutum bakwai a ranar Alhamis.

Sojojin da ke sintirin sun kuma cafke wani dan garin Shinkafi dauke da makudan kudade a wani shingen binciken ababen hawa.

Ya ce da aka titsiye shi, sai aka gano cewa cewa mai sayen shanun sata a hannun ’yan bindiga ne.

“Zuzzurfan bincike ya gano cewa mutumin na hada baki da ’yan bindiga, yana hannunmu za a ci gaba da aiki.

“Sojoji sun yi amfani da bayanan sirri kan ’yan bindigar da suka kai hari a kauyen Kimbisawa a Karamar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina, inda nan take suka kai dauki suka kubutar da mata biyu da karamin yaro daga hannun ’yan bindiga suka kuma damka su ga iyalansu,” inji Enenche.

Ya kara da cewa a ranar ce sojoji suka bindige wani mahari da daga cikin ’yan bindigar da suka yi musu kwanton bauna a lokacin da suke sintiri a hanyar Batsari zuwa Jibia.

“An kashe dan bindiga daya, dayan kuma ya ranta a na kare da raunin bindiga,” inji shi.