✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji Sun Mika Daliban Chibok 3 Da Aka Ceto Ga Gwamnatin Borno

Kwamandan rundunar ‘Operation Hadin Kai’ a yankin Arewa maso Gabas, Manjo-Janar Christopher Musa, ya mika daliban makarantar Chibok uku da ’ya’yansu hudu da aka kubutar…

Kwamandan rundunar ‘Operation Hadin Kai’ a yankin Arewa maso Gabas, Manjo-Janar Christopher Musa, ya mika daliban makarantar Chibok uku da ’ya’yansu hudu da aka kubutar daga hannun ’yan Boko Haram tun shekara takwas da suka gabata.

Biyu daga cikinsu, Kauna Luka mai shekara 25 da Ruth Bitrus mai shekara 24 suna da ’ya’ya guda-guda, sai kuma Hanatu Musa mai shekara 26 ta haifi ’ya’ya biyu.

Hanatu tana da shekaru 18, Kauna shekaru 17, Ruth kuma shekaru 16 a lokacin da ’yan ta’adda suka sace su a makarantarsu da ke karamar hukumar Chibok a Jihar Borno.

Janar Musa ya bayyana wa manema labarai cewa kawo yanzu ’yan ta’addan Boko Haram 70,593 ne suka mika wuya ga sojoji.

Ya ce, “Halin tsaro gaba daya a fadin Arewa maso Gabas ya kasance abin da ba za a iya hasashensa ba, domin tun daga lokacin da aka fara daukar mataki na musamman na Operation DESERT SANITY da Operation LAKE SANITY, ’yan ta’addan sun sallama har ta kai ga ba za su iya ci gaba da gudanar da ayyukan yaki kamar yadda suka saba a baya ba yadda suke cin karensu babu babbaka ba.

“Sakamakon ci gaba da ayyukan da sojojin suka yi, da yawa daga cikin ’yan ta’addan da aka lalata sansanoninsu da matsuguninsu a lokacin aikin share fage na baya-bayan nan sun ci gaba da yin kaura daga wannan yanki zuwa wani yanki.

“Shiga yanayin damina ya kawo musu nakasu yadda ala tilas suke barin wasu wuraren sakamakon fatattakar su da ake yi daga yankunan da suke jin dadi.

“Duk da haka, ’yan ta’addar sun ci gaba da hada abubuwan fashewa da suke kai hare-haren a kan wasu kebabbun al’ummomi da ke sauran wurare.