✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun mika ’yan matan Chibok 2 ga gwamnatin Borno

Kowacce daga cikinsu na dauke da dan da ta haifa

Rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai da ke yankin Arewa maso Gabas ta mika wasu ’yan matan makarantar Chibok biyu da aka kubutar daga hannun Boko Haram tun shekaru tara da suka gabata.

Kwamandan rundunar, Manjo Janar Christopher Musa ne ya mika Hauwa Joseph da Maryam Dauda ga gwamnatin ranar Talata a Maiduguri, babban birnin Jihar.

Boko Haram dai ta sace ’yan matan sama da 200 ne a makarantar Sakandaren Gwamnati da ke garin Chibok a Jihar Borno a ranar 14 ga Afrilun 2014.  .

Ko wace daga cikin ’yan matan da aka ceto na dauke da jariri mai kimanin shekara daya da rabi.

Aminiya ta gano cewa an sake aurar da matan ga wasu ’yan ta’adda bayan da sojoji suka kashe mazajensu na farko.

Da yake karin haske ga manema labarai a hedkwatar rundunar ta Maimalari, Kwamanda Manjo Janar Musa ya ce, ana kokarin ganin an ceto sauran ’yan matan Chibok da kuma duk wadanda ke hannun ’yan ta’adda masu aikata laifuka a yankin.

Ya ce, “Na yi farin cikin sanar da ku wasu daga cikin manyan nasarorin da sojojin wannan rundunar ta Operation HADIN KAI ta samu a hare-haren da suke kai wa kan wadannan ’yan ta’adda na Boko Haram da ISWAP.

“Baya ga ceto wadannan ’yan matan na Chibok guda biyu da ’ya’yansu, mun kuma kashe ’yan ta’adda da dama da suka fake a dajin Sambisa, musamman ma Timbuktu, a lokacin da muke sintiri na yaki a kai a kai.

“Yayin da damina ta shiga kuma manoma da yawa ke son zuwa gonakinsu, za mu yi bakin kokarinmu wajen samar da tsaro ga manomanmu a harkokin noman su, amma muna so mu yi kira ga manoman su yi hattara da wasu abubuwan fashewa da aka dasa  a wasu yankunan, duk da cewa sojoji na yin duk mai yiwuwa don ganin sun share mafi yawan wuraren da ake zargin akwai bama-bamai da ‘yan ta’addan suka dasa a yankin,” inji Kwamandan.