✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun shirya gasar kwallon kafa ta zaman lafiya a Kudancin Kaduna

Rundunar ta shirya gasar ce don samar da zaman lafiya

Kungiyar Kwallon Kafa ta Zonkwa Selected dake Karamar Hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna, ta lashe gasar kwallon kafa ta zaman lafiya da rundunar kiyaye zaman lafiya ta Operation Safe Haven ta shirya a Kudancin Kaduna.

Kungiyar dai ta lashe gasar ce bayan ta lallasa takwararta ta Golden Balley da ke Karamar Hukumar Jama’a da ci 3-1 a wasan karshe da aka buga a sabon filin wasa na garin Kafanchan a da ke Jihar ta Kaduna.

Da yake jawabi bayan kammala gasar, Kwamandan Rundunar ta OPSH mai hedkwata a Jos, babban birnin Jihar Filato, Manjo Janar Ibrahim Sallau Ali, ya ce sun shirya ta ne domin bai wa matasa damar nuna bajintarsu tare da kara musu dankon zumunci baya ga tallafa musu da kudi don samun abin yi.

Janar Ali, yace harkar wasanni na daya daga cikin abubuwan da aka yi amanna suna kara dankon zumunci tsakanin matasa, inda ya ce hakan ne yasa suka shirya gasar don kungiyoyin kwallon kafa daga Kananan Hukumomi biyar da ake yawan samun tashin hankali a Kudancin Kaduna.

“Mun yi imani cewa zaman lafiya mai dorewa za a same shi ne kawai idan an shigo da duk wani mai ruwa da tsaki cikin lamarin musamman matasa tare da sama musu abin dogaro.

“Hakan ne yasa muka janyo matasa tare da shirya musu wannan gasar baya ga sauran abubuwa da muke yi na farfado da zaman lafiya,” inji shi.

Ya kuma yaba wa rundunarsa da ke barikin soji na Kafanchan karkashin jagorancin Kanar Timothy Opurum da suka samar da zaman lafiyar da ya ba da damar buga wasan ba tare da tashin hankali ba.

Rundunar, tare da hadin gwiwa da cibiyar Beautiful Gate Handicap da ke garin Jos sun raba kekunan guragu guda 30 ga guragun da aka zakulo daga Kananan Hukumomin biyar.

Kungiyar kwallon kafa ta Kagoro Utd da ke Karamar Hukumar Kaura ce ta zo ta hudu inda aka basu cek na N200,000 sai kungiyar kwallon kafa ta Gwantu United daga Karamar Hukumar Sanga ta zo ta uku inda aka basu kyautar N300,000 yayinda Golden Balley da ke Karamar Hukumar Jama’a ta zo ta biyu tare sa samun kyautar N500,000 sai zakarun gasar, Zonkwa Selected da aka ba kyautar N700,000.

Kungiyar da tafi kowacce ita ce Jama’a Emirate FC sai Bogoro Alkali daga karamar hukumar Kauru ya samu kyautar wanda yafi zura kwallaye (bayan ya zura kwallaye 5), yayinda Kumai daga karamar hukumar Kaura aka bashi kyautar dan wasa mafi ladabi.

Baba Audu daga karamar hukumar Jama’a ne aka ba kyautar dan wasa mafi bajinta (Best Player).

Daga cikin manyan bakin da suka halarci gasar akwai Kwamishinan Raya Yankin Kafanchan; Misis Phoebe Sukai Yayi da Kwamishinan Wasanni na Jihar Kaduna shugabannin kananan hukumomin Jama’a da Sanga da Kauru da Sarkin Jama’a; Alhaji Muhammadu Isa Muhammadu da wakilan Sarakunan Zikpak da Chawai da Attakar da Kaninkon da shugabanin jami’an tsaro na ’yan Sanda da na Sibil Difens da na Hukumar Kiyaye Hadura da ’yan bijilenti na KADVS da sauransu.