✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun tsare jarumin Nollywood, Chinwetalu Agu, kan IPOB

An kama dan fim din kan alaka da IPOB ne a garin Onitsa, Jihar Anambra.

Sojoji sun kama fitaccen dan wasan fina-finan masana’antar Nollywood Chiwetalu Agu a Anambra saboda zargin sa da alaka da haramtacciyar kungiyar IPOB.

A ranar Laraba ne sojoji suka cafke tauraron na Nollywood, Chinwetalu Agu, saboda sanya kayan Biafra a sanannen unguwar Upper Iweka da ke garin Onitsha na Jihar Anambra.

Aminiya ta gano cewa tauraron na Nollywood ya je garin Onitsa ne domin rabon kayan tallafin kayan abinci ga mabukata.

Wani bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda sojoji suka kama Agu suka sa shi a cikin mota sannan suka wuce da shi, a yayin da yake sanye da tufai masu dauke da launin tutar IPOB.

Wani dan wasan Nollywood da ya nemi a boye sunansa ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da take hakkin dan Adam.

“Chinwetalu Agu yana danganta kansa da Biafra, musamman ma kayansu. Wani abokina soja ya kira ni mintoci kadan da suka wuce ya sanar da ni halin da ake ciki, cewa Chinwetalu Agu yana hannunsu, ” in ji shi.

Jami’an tsaron Najeriya sun hana mutane amfani da kayan Biafra.

Mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya ce rundunar na sane da lamarin amma har yanzu ba ta samu cikakken bayani ba.