✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun yi bore kan rashin isassun makamai

Sun yi bore saboda rashin biyan su alawus dinsu da kuma karancin kayan yaki

Rahotanni sun ce sojojin Rundunar Operation Lafiya Dole sun yi bore kan tura su fagen yaki da ’yan ta’addan Boko Haram ba tare da isassun makamai ba.

Majiyoyi daga Barikin Soji Maimalari a Maiduguri, Jihar Borno sun ce sojojin sun mamaye hedikwatar Operation Lafiya Dole ranar Alhamis da dare suka rika harbi a sama.

Sun bayyana cewa sun dauki matakin ne saboda rashin biyan su alawus dinsu da kuma rashin samar musu da isassun kayan yaki.

Wasu sojojin da suka nemi a sakaya sunayensu, sun ce mayakan Boko Haram sun hallaka wasunsu a harin da aka kai musu a garin Marte saboda makaman ’yan ta’addan sun fi nasu.

Gidan Talabijin na Channels ta ruwaito cewa kakakin Rundunar Operation Lafiya Dole, Kanar Isa Ado, ya tabbatar da labarin.

Boren sojojin na zuwa ne ’yan kwanaki bayan fallasan da Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Babagana Munguno ya yi cewa an nemi kudin sayen makamai da aka bayar karkashin tsoffin Hafsoshin Tsaro an rasa.

Monguno ya yi zargin cewa wasu kudaden da aka bai wa tsoffin hafsoshin tsaro na sayen makamai don karfafa yaki da Boko Haram sun yi layar zana.

Amma mai magana da yawun Shugaban Kasa, Garba Shehu, ya bayyana cewa ba zai yiwu a ci kudin makamai a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari ba.

Shehu ya bayyana hakan ne a shirin ‘Politics Today’ na gidan Channels, inda ya ce Dala biliyan daya aka saki a 2018 don sayen makamai.