✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Mali

Karar harbe-harben bindiga a kusa da wani babban sansanin sojojin da ke dab da babban birnin kasar Mali na Bamako a ranar Talata ya jefa…

Karar harbe-harben bindiga a kusa da wani babban sansanin sojojin da ke dab da babban birnin kasar Mali na Bamako a ranar Talata ya jefa tsoro a kasar da dama ake zaman dar-dar.

Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa sojoji ne suka yi harbe-harben a sansanin da ke garin Kati, kimanin nisan kilomita 15 daga Bamako.

Wani soja a sansanin ya tabbatar wa da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa yinkuri ne na wasu sojoji domin nuna bacin rai kan abubuwan da ke faruwa a kasar.

“Muna bukatar canji,” inji majiyar.

Lamarin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan adawa ke kokarin dawowa da zanga-zangar kin jinin shugaban kasar, Ibrahim Boubacar Keita.

Masu zanga-zangar dai sun taru a Dandali Kwatar ‘Yanci na Bamako inda a cikinsu wasu ma suka yi kokarin fasawa tare da sace kayyakin Ofishin Ministan Shari’ar kasar da ke dab da dandalin.

To sai dai tuni ofishin Ministan Tsaron kasar ya shaida wa AFP cewa gwamnati na bin lamarin a hankali kuma tana dab da shawo kan lamarin.

Kasar Mali dai ta kasance cikin halin zaman dar-dar tun watan Yuni lokacin da zanga-zangar neman shugaba Boubacar ya sauka daga mukaminsa ta fara.

Yunkurin juyin mulkin na zuwa ne a ranar da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya saurari jawabin Manzo na Musamman na kungiyar ECOWAS, Tsoho Shugaba Goodluck Jonathan kan hanyoyin magance matsalolin rikicin na Mali.

Ko a farkon watan Agusta Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta aike da tawagar shiga tsakani karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan domin kawo karshen dambarwar siyasar kasar.