✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojojin Amurka 6,000 za su taimaka wajen kwaso mutane daga Afghanistan

Amurka ta ce wadanda za ta kwaso sun hada da 'yan kasarta da na kawayenta.

Shugaban Amurka, Joe Biden ya ba da umurnin tura sojoji 6,000 zuwa Afghanistan don su taimaka wajen kwaso ’yan kasarta, da na kawayenta da kuma abokan huldarta da ke son ficewa.

Ya bayyana hakan ne yayin wani jawabi ga manema labari ranar Litinin a Fadar White House, inda ya ce dakarun na kokarin tsare filin jirgin saman kasa da kasa na Hamid Karzai da ke Kabul domin a kwashe su cikin sauki.

Biden ya ce, “Nan ba da jimawa ba za mu kwaso dubban Amurkawan da suke rayuwa da aiki a Afghanistan, sannan mu taimaka wajen kwaso yan kasashe kawayenmu daga kasar.

“Kazalika, sojojin Amurka za su taimaka wajen ba da izinin shiga kasarsu ga ’yan gudun hijira ’yan Afganistan domin su taimaka musu wajen ficewa daga kasar.

“Akwai wadanda sun cancanchi fita daga kasar, kuma za mu taimaka wajen fitar dasu.

“Dakarun Amurka za su nuna kwarewa wajen wannan gagarumin aikin, duk da cewa mun san akwai hatsari matuka a cikinsa.

“Mun fada wa ’yan Taliban cewa duk wanda ya kawo wa dakarunmu hari wajen hana wannan aikin, Amurka za ta nuna karfin da take da shi a kansa.

“Za mu kare mutanenmu da duk karfin da muke da shi idan hakan ta kama,” inji Biden.

Shugaban ya kuma ce ba zai tilasta wa sojojin kasarsa ci gaba da yakin da ba nasu ba, inda ya ce wannan yakin basasar da ke ci gaba da daukar rayukan jama’a ana zubar da jini, wanda ba a san ranar karewarsa ba, ba nasu ba ne.

“Wannan yakin bai shafi bukatar kasarmu ba, kuma ba shi Amurkawa ke so ba,” inji Shugaba Biden lokacin da yake kare matsayin Amurka kan janye dakarunta daga Afghanistan.