✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojojin Amurka sun fice daga Afghanistan

Taliban ta sanar da samun nasara kan Amurka a Afghanistan.

Mutanen kasar Afghanistan sun wayi garin ranar Talata a karkashin cikakken ikon Taliban bayan dakarun Amurka sun janye daga kasar.

A ranar ce kakakin Taliban, Zabihullah Mujahid ya sake sanar da alkawarin kungiyar na kare kasar da bude filin jirgi ba da dadewa da kuma yin afuwa ga tsoffin abokan gabarsu.

“Sojojin Amurka sun fice da filin jirgin Kabul, kuma kasarmu ta samu cikekken ’yancinta,” inji Zabihullah Mujahid a taron ’yan jarida da ya gudanar a Filin Jirgin Hamid Karzai da ke birnin Kabul.

Dakarun runduna ta musamman ta “Badri 313” ta kungiyar ne suka raka Mujahid zuwa filin jirgin, ’yan sa’o’i bayan janyewar dakarun na Amurka.

An yi bikin janyewar dakarun na Amurka ne a cikin dare, wanda Taliban ta ayyana a matsayin gagarumar nasara a gare ta.

“Taliban ta sha bayyana yakinta da sojojin kasashen da suka mamaye Afghanistan a matsayin hakki domin samar wa kasar cikakken ’yanci,” inji wakilin kafar yada labarai ta Aljazeera a birnin Kabul, Charles Stratford.

A wani jawabi da ya yi wa dakarun Badri 313 kai tsaye ta intanet, Zabihullah Mujahi ya ce, “Ina fata kun shirya tsaf domin kula da kasarmu, ganin yadda ta yi fama da yaki da mamayar kasashen Yamma da kuma gajen hakurin mutane.”

Da aka tambaye shi game da yiwuwar kafa gwamnatin riko a kasar, Zabihullah ya yi watsi da batun, yana mai cewa, “Za a samu cikakken tsaro a Kabul, mutane su kwantar da hankalinsu.”

A halin da ake ciki Taliban ta saki fitacciyar ’yar siyasa mai kare hakkin mata da ta tsare a gida, Fawzia Koofi, har ta isa kasar Qatar, inda za ta hadu da iyalanta.

Kungiyar na kuma tattaunawa da kasashen Turkiyya ta Qatar kan gudanar da filin jirgi na Kabul ta yadda baki za su samu ficewa daga Afghanistan a jiragen fasinja.

Birtaniya ta ce har yanzu akwa ragowar daruruwan ’yan kasarta a Afghanistan da ba a kwaso ba.

Amurka kuma ta sanar cewa duk da cewa ta janye daga Afghanistan, ofishinta da ke Doha a kasar Qatar zai ci gaba da aiki domin taimakon ’yan kasarta da iyalansu da ke a Afghanistan.