✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojojin Amurka sun kashe Shugaban Kungiyar ISIS

Shugaban ISIS al-Quraishi ya tayar da bam ya kashe kansa bayan sojojin Amurka sun kai masa samame

Shugaban Kasar Amurka, Joe Biden, ya sanar da cewa sojojin kasar sun hallaka Shugaban Kungiyar IS, Abu Ibrahim al-Hashim al-Quraishi, a wani samame da suka kai a yankin Arewa maso Yammacin Siriya.

Shugaba Biden, ya ce sojojin sun yi nasarar kashe Abu Ibrahim al-Quraishi ne a wani samame da suka kai tare da mayakan Kurdawa a yankin Idlib da ke Siriya.

Kamfanin Dillacin Labaran Faransa, ya rawaito wani jami’in gwamnatin Amurka na cewa Quraishi ya tayar da bam ne, inda ya hallaka kansa lokacin kai harin dakarun suka kai mishi.

Biden ya ce sakamakon umarnin da ya bayar a ranar Laraba, dakarun sojin Amurka sun yi nasarar kai samamen yaki da ta’addanci domin kare lafiyar Amurkawa da kawayensu tare da tabbatar da zaman lafiya a duniya.

Shugaban ya jinjina wa kwarewar sojojin da suka kawar da Abu Ibrahim al-Hashimi al-Quraishi, Shugaban Kungiyar ISIS.

Idan ba a manta ba al-Quraishi, wanda aka fi sani da Amir Mohammed Said Abd al-Rahman al-Mawla, shi ne mutumin ya maye gurbin tsohon Shugaban Kungiyar ISIS, wato Abubakar al-Baghadadi, wanda sojojin Amurka suka kashe a Iraki, a watan Oktoban shekarar 2019.