✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojojin Burkina Faso sun kashe fararen hula ta sama ‘bisa kuskure’

Sai dai ba a bayyana yawan mutanen da aka kashe din ba

Rundunar Sojin Kasa ta Burkina Faso ta dauki alhakin kisan wasu fararen hula da ta ce dakarunta sun yi bisa kuskure a wasu jerin hare-hare da suka kai ta sama.

A ranar Litinin ce dai sojojin suka kai harin a Kudu maso Gabashin kasar.

Kasar dai na fama da ’yan tawaye ne masu dauke da makamai da ke da alaka da kungiyoyin ISIS da Al-Qa’ida, wadanda ke iko da bangarori da dama na kasar.

A cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar ranar Laraba, sun ce, “A yayin hare-haren da muka kai ta sama da suka ba mu damar hallaka ’yan ta’adda da dama, an sami akasin kashe fararen hula bisa kuskure.”

Sai dai rundunar ba ta bayyana adadin fararen hular da lamarin ya shafa ba.

Rahotanni sun ce an kashe mutanen ne a tsakanin garuruwan Kompienga da Pognoa, da ke kusa da kan iyakar kasar da Togo, a ranar Litinin.

Ita kanta kasar ta Togo da ke fama da gyauron masu tayar da kayar bayan na Burkina Faso, sai da ta kashe kananan yara bakwai da ba su ji ba, ba su gani ba a watan da ya wuce a kusa da kan iyakar.