✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojojin Habasha sun kwace wasu yankuna daga ’yan tawayen Tigray

Rikicin dai ya jefa kasar cikin matsananciyar bukatar agaji.

Kasar Habasha ta tabbatar da cewa sojojin ta sun kwace iko da wasu yankuna da ’yan tawayen Tigray ke iko da su a Arewacin kasar, ciki har da garuruwan Kobo da Waldia.

Fadan dai wanda ake ci gaba da fafatawa tsakanin dakarun da ke biyayya ga Firaminista Abiy Ahmed da na Masu Fafutukar ’Yanto Yankin na Tigray (TPLF), dai ya kuma jefa kasar cikin matsananciyar bukatar tallafi, ta yadda sai da Majalisar Dinkin Duniya ta ba da umarnin bincike kan zargin cin zarafin bil Adama.

Rikicin dai ya haifar da mummunan fada tsakanin bangarorin biyu na tsawon wata 13, kuma dubban mutane ne suka rasa rayukansu a sanadinsa.

An dai yanke hanyoyin sadarwa a yankin kuma hatta ’yan jarida an takaita wuraren da suke iya shiga, lamarin da ya sa yake da matukar wahala a iya tabbatar da ainihin abin da ke faruwa a yankin.

To sai dai a ranar Asabar, kamfanin sadarwa na gwamnatin kasar ya ce dakarun gwamnati sun sami nasarar kwato garuruwan Sanqa da Sirinqa da Waldia da Hara da Gobiye da Robit da kuma Kobo.

“Mun tilasta wa abokan gabarmu tserewa saboda luguden wuta daga dakarunmu,” inji gwamnatin a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook ranar.

Tun daga watan Oktoba dai, bangarorin biyu sun sami nasarar karbe iko da birane da dama, inda birane suka yi ta canza hannu tsakaninsu.

Ko a ranar Lahadi, ’yan tawayen sun kwace wata cibiyar tarihi ta hukumar UNESCO da ke Lalibela, kwana 11 bayan dakarun gwamnati sun yi ikirarin kwaceta daga TPLF.