✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojojin Isra’ila sun kashe Bafalasdine, sun jikkata wasu mutum 13

Ko a watan azumin Bara dai sai da isra’ila ta kai makamancin wannan hari a masallacin Kudus

Sojojin Isra’ila sun kashe wani Bafalasdine a wani sansanin ’yan gudun hijira na Jenin da ke Gabar Yammacin Kogin Jordan, sannan suka jikkata wasu mutum 13.

Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta ce daga cikin wadanda harin ya ritsa da su har da wata budurwa da aka harba a ciki a harin na birnin Tel Aviv.

Rahotanni sun ce Bafalasdinen da aka kashe sunan shi Ahmad al-Saadi, kuma mamba ne kungiyar masu fafutukar jihadi ta Saraya al-Quds.

Sojojin na Isra’ila sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa suna ci gaba da kaddamar da hare-haren soji a sansanin na Jenin.

Yankin Jenin dai wani babban jigo ne a yankunan Falasdinawan.

Bugu da kari, sojojin na Isra’ila sun kuma mamaye wani kauye mai suna Burqin da ke kusa da Jenin din, inda suka raunata mutum biyu, a yunkurinsu na kama wani tsohon fursuna, Nour al-Din Hamada.

Daga ranar 22 ga watan Maris din da ya gabata zuwa yanzu dai, an kashe mutum 14 a hare-haren da aka kai a Isra’ila, ciki har da wasu da kungiyar ISIS ta kai.

A tsakanin lokacin kuma, an kashe Falasdinawa kusan 10.

Ko a watan azumin Ramadan na bara dai sai da sojojin na Isra’ila suka kai hari kan Musulmai masu ibada a masallacin birnin Kudus, bayan shafe kwana 11 suna kai hare-hare a masallacin.