✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa 54 —MDD

Falasdinawan da aka kashe a wata takwas sun ninka na 2020 sau biyu.

Jami’ar Kare Hakki ta Majalisar Dinkin Duniya, Michelle Bachelet, ta ce sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa 54, ciki har da kananan yara 12 daga farkon shekerar 2021 zuwa yanzu.

Bachelet ta bayyana hakan ne yayin bude Babban Taron Hukumar Kare Hakki ta Majalsiar Dinkin Duniya (UNHRC) karo na 48 a birnin Geneva na kasar Switzerland.

“Kawo yanzu a wannan shekara, Falasdinawa 54 da suka hada da kananan yara 12 ne sojojin Isra’ila suka kashe a Gabar Yammacin Kogin Jordan,’’ a cewar Bachelet.

Ta ce yawan mutanen da sojojin na Isra’ila suka kashe ya ninka wadanda aka kashe a 2020 sau biyu, sannan sun yi wa akalla mutum 1,000 raunin harbi

Sai dai ta ce, “Na damu matuka game da murkushewar da Gwamantin Falasdina ke yi wa masu tayar da kayar baya a ’yan watannin nan.

“A zanga-zangar da ta kai ga kashe dan gwagwarmaya Nizar Banat a watan Yuni, jami’an tsaron Palasdinawa sun yi amfani da karfi fiye da kima a kan masu zanga-zangar lumana,’’ inji ta.

Ta ce yawan masu fafutika da aka tsare a cikin watan Agusta ya kara tabbatar da amfani da karfin tuwo a kansu, don haka ta yi gira ga hukomin da su tabbatar da kare hakkin masu zanga-zanga da sauran hakkokin bil Adama.

A ranar Litinin aka fara babban taron na UNHRC karo na 48, wanda za a kammala ranr 8 ga watan Oktoba, 2021.