Sojojin Najeriya sun kera jirgin ruwa na yaki | Aminiya

Sojojin Najeriya sun kera jirgin ruwa na yaki

Jirgin ruwa na yaki da rundunar ta kera
Jirgin ruwa na yaki da rundunar ta kera
    Sani Ibrahim Paki

Rundunar Sojojin Ruwa ta Najeriya ta kammala shirye-shiryen kaddamar da jirgin ruwa na yaki da injiniyoyinta suka kera.

Wannan dai shi nekaro na uku da rundunar take kera jirgin yaki a cikin gida.

Injiniyoyin rundunar ne dai suka jagoranci aikin kera jirgin, bisa kulawar kamfanin Navy Dockyard Limited, mallakin rundunar da ke unguwar Victoria Island a Jihar Legas.

Ana dai sa ran jirgin zai taimaka wajen yakin da ake yi da ’yan fashin teku a gabar ruwan sassa daban-daban na kasar nan.

Kazalika, jirgin zai taimaka matuka wajen yaki da kowacce irin barazanar tsaro da kasar za ta iya fuskanta musamman a kan iyakokinta na ruwa.