✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojojin Sudan za su cire hannunsu a harkokin siyasa

Sojojin kasar Sudan sun ce za su tsame hannunsu daga harkokin siyasa bayan zaben kasar da za a gudanar a shekarar 2023. Shugaban sojojin kasar,…

Sojojin kasar Sudan sun ce za su tsame hannunsu daga harkokin siyasa bayan zaben kasar da za a gudanar a shekarar 2023.

Shugaban sojojin kasar, Janar Abdel Fattah al-Burhan, shi ne ya sanar da hakan yana mai cewa ba za a ba wa tsohuwar jam’iyya mai mulkin kasar kowace irin dama ba a gwamnatin rikon kwaryar kasar.

Janar Burhan ya shaida wa kamfanin dillanci labarai na Reuters cewa tsohuwar jam’iyya mai mulki ba za ta shiga gwamnatin rikon kwaryar ba, kuma sojoji za su janye hannunsu daga harkokin siyasa bayan zaben na 2023.

“Idan har aka zabi gwamnati, maganar gaskiya ita ce, bai kamata sojoji ko jami’an tsaro su shiga harkokin siyasa ba,” inji shi.

Juyin mulkin da Burhan ya yi wa gwamnatin hadakar jam’iyyu bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar, Omar al-Bashir, ya sha suka daga ciki da wajen Sudan, musamman kan yadda aka tsare manyan jami’an gwamnati da kuma murkushe masu zanga-zanga.

Jami’an lafiya sun ce akalla masu zanga-zanga 44 ne suka rasu, yawancinsu sakamakon raunin harbi daga jami’an tsaro.

A watan Oktoba ne ya yi juyin mulkin da ya kawo tsaiko ga mulki dimokuradiyya a Sudan, lamarin da ya sa dubban mutanen kasar yin bore tare da nema kira da sojoji su cire hannunsu a harkokin siyasa.

Daga baya a watan Nuwamba sojojin suka kulla yarjejeniyar dawo da Fira Minsita Abdalla Hamdok kan kujerarsa zuwa zaben watan Yuli a 2023.

Amma bayan kulla yarjejeniyar, kungiyoyin da jam’iyyun siyasara kasar sun ce dole sojoji su janye hannunsu a harkokin siyasa nan take kuma ba su yarda da duk wata yarjejeniya da sojojin suka kulla da Fira Minista Hamdok ba.