✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojojin Ukraine 1,000 sun mika wuya a Mariupol —Rasha

Hafsoshin soji 162 da mata 47 da wasu akalla 100 da suka samu raunuka sun yi saranda.

Gwamnatin Rasha ta yi ikirarin cewa sojojin Ukraine sama da 1,000 sun mika mata wuya a yankin Mariupol da dakarun Rasha suka mamaye na tsawon sama da wata guda a Gabashin Ukraine.

Ma’aikatar Tsaron Rasha ta yi wannan ikirarin ne a ranar Laraba, inda ta ce daga cikin sojojin Ukraine din da suka mika wuya akwai hafsoshi 162 da mata 47 da wasu akalla 100 da suka samu raunuka.

“Sojojin Ukraine 1,026 sun ajiye makamansu sun mika wuya a kusa da masana’antar sarrafa tama ta Metallurgical”, inji sanarwar da Rasha ta fitar.

Ana zargin Rasha tana kokarin hade yankin Crimea da ta mamaye da yankunan Donetsk da Lugansk da ke Donbas da suke neman ballewa daga Ukraine, kuma tun farkon mamayarta a Ukraine ta kafa wa Mariupol kawon zuka.

Ana hasashen an kashe dubban fararen hula a Mariupol, inda aka gwabza kazamin fada tsakanin sojojin Rasha da na Ukraine.