✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Solskjaer ya tsawaita kwantaraginsa a Manchester United

Kocin zai ci gaba da zama a kungiyar har zuwa 2024.

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya tsawaita zamansa a kungiyar zuwa karshen kakar wasanni ta 2024.

Hakan ya biyo bayan kokarin da kocin ya yi a kakar wasannin da aka kammala ta 2021/2022, inda Manchester United din ta kare a mataki na biyu a gasar Firimiyar Ingila, sannan ta je wasan karshe na gasar Europa.

Manchester ta dauki Solskjaer a matsayin kocin rikon kwarya a watan Disambar 2018, bayan sallamar Jose Mourinho da ta yi.

Kungiyar ta yi rashin nasara a wasan karshe na gasar Europa a hannun kungiyar Villarreal daga bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Solskajer ya buga wa Manchester United wasa daga 1996 zuwa 2007, inda ya zura kwallaye 126, mafi shahara daga ciki shi ne a wasan karshe na Gasar Zakarun Turai ta 1999.