✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Southampton ta sayi dan wasan Najeriya Joe Aribo

Southampton ta ce sun cefano dan wasan tsakiyar ne daga kungiyar Rangers ta Scotland.

Kungiyar kwallon kafar Southampton da ke gasar Firimiyar Ingila ta rattaba hannu kan kwantaragin shekaru hudu da dan wasan Najeriya, Joe Aribo.

Sanarwar da mahukuntan kulob din Southampton suka fitar a ranar Asabar ta ce sun cefano dan wasan tsakiyar ne daga kungiyar Rangers ta Scotland.

Kawo yanzu kungiyoyin kwallon kafa na Rangers da Southampton ba su bayyana kudin da aka yi ciniki dan wasan ba, amma wasu jaridu a Burtaniya na cewa kudaden sun haura Dala 7,000.

Aribo mai shekaru 25 da aka haifa a birnin Landan ya nuna bajinta a zamansa na Rangers, inda a wasanni 150 ya zura kwallaye 26 sannan ya taimaka wa kulob din lashe kofin babbar gasar kwallon kafar Scotland.