✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Squid Games: Fim din Netfilx mafi shahara a duniya

Cikin mako guda mutum miliyan 111 sun kalli shirin.

‘Squid Games’ ya zama fim din da ya fi shahara da daukar hankalin masu kallo a fadin duniya a kafar Netfilx.

Squid Gwames, wanda aka saka a Netflix ranar 17 ga watan Satumba, 2021, fim ne mai dogon zango wanda ’yan kasar Koriya ta Kudu suka shirya, Nexflix kuma ya dauki nauyinsa.

Hwamg Dong-hyuk shi ne daraktan fim din, wanda ya karya tarihin daukacin fina-finan Netflix a cikin kwana 30 kacal.

An shirya fim din ne a kan tsarin wani wasan yara a kasar Koriya ta Kudu, inda aka gayyato mutane da bashi ya yi musu katutu domin su fafata a wata gasa.

An gasar, an sanya kyautar biliyan Dala 45.6 ga duk wanda ya zama gwarzo (Lee Jung-jae), kuma fara gasar ke da wuya aka fara tataburza a tsakanin jaruman.

Squid Games
Squid Games

Bayan sakin shirin da mako guda ya kafa tarihi, inda aka kalle shi sau miliyan 111 a fadin duniya, sama da shirin ‘Bridgertin’.

Squid Games ya ci gaba da daukar hankalin masu kallo inda ake ta tattaunawa tare da muhawara a kansa a kafafen sada zumunta.

Tuni masu amfani da kafafen sada zumunta kamar masu wasannin barkwanci, suka shiga kwaikwayon shirin ta hanyar yin irin shigar da ’yan wasan ke yi da sauransu.

Dong-hyuk (daraktan shirin) ya bayyana cewa tun shekara 10 da suka gabata ya tsara shirin amma rashin mai daukar nauyi ya hana shi fara dauka.