✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sterling Bank ya bunkasa harkar noma a Najeriya —Awosanya

Bankin kasuwanci na Sterling Bank na taimaka wa manoma domin samun riba

A yunkunrinsa na karkata ga bangaren zuba jari na a fannin lafiya, ilimi, noma, makamashin zamani da sufuri (HEART), bankin kasuwanci na Sterling Bank ya bullo da shiri na musamman a radiyo domin bunkasa amfani da binciken kimiyya da sabbin ilimi a bangaren noma ta hanyar wayar da kan manoma.

Shirin ‘Farmers Radio’ ya kuma samar da fagen wanzajjen tattaunawa ga masu ruwa da tsaki a bangaren noma.

A hirar da aka yi da Janar-Manajan ba da Rancen Noma da Hakar Ma’adanai na Sterling Bank, Bukola Awosanya, ta bayyana manufar shirin da nasarorin da ya samu.

 

Mene ne hikimar bullo da shirin ‘Farmers’Radio’ a Najeriya?

A matsayinmu na bankin da ya damu da kawo cigaba da bunkasar tattalin arzikin Najeriya da ’yan kasar, mun yi la’akari da tasirin bangarorin noma da tattalin arziki ga rayuwar mutane wurin samar da ayyuka da kuma bunkasa karfin kayan da ake samarwa a cikin gida (GDP).

Sai muka ga dacewar mu karfafa harkar kasuwancin noma domin samar da wadataccen abinci a gida da kuma rage shigo da kaya daga ketare ta hanyar bullo da sabbin hanyoyin samun kudaden shiga daga kasashen waje.

Saboda haka sai muka fara da bullo da tsarin wayar da kansu game da sabbin dabarun noma, bunkasar rayuwar manoma, da kuma kara yawan amfanin da suke girbewa.

Mun yi amannar cewar hakan zai yi nasara ne idan aka yi amfani da wata kafar da mutane ke yawan sauraro – bincikenmu ya gano cewa radiyo ne kafa mafi dacewa.

Makasudin ‘Farmers’ Radio’ shi ne bunkasa ilimi da kwarewar manoma domin samar da nagartaccen amfanin gona mai yawa ga kamfanoni; kyautata alaka tsakanin masu ruwa da tsaki; gano bukatun masu masana’antun kayan gona, kungiyoyin manoma; sanya kudi domin magance matsaloli; da kuma wayar da kan matsakaitan manoma.

‘Farmers’ Radio gudunmuwa ce daga Sterling Bank domin kyautata tsare-tsaren da za su yi tasiri wajen bunkasa harkar noma a cikin gida da kuma ketare.

Duk da cewa shirin na radiyo ne ‘Farmers’ Radio’ ya zama fagen tattaunawar masu ruwa da tsaki – kungiyoyin manoma, masu sayar da kayan noma, masu masana’antu – domin gano irin damar da bangaren ke da ita da kuma hanyoyin magance matsaloli.

 

Yaya kike ganin karbuwar shirin a wurin wadanda aka bullo da shirin dominsu?

Manoman sun yi maraba da shirin, wanda ya fi mayar da hankali kan kanana da matsakaitan manoma na karkara.

Sauran masu ruwa da tsaki ma na ganin shi a matsayin wata dama ce ta tattaunawa game da kayan noma da sauran bukatun manoma.

Shirin ya karbi bakuncin Shugaban kamfanin taraktoci na Mahindra; Shugaban kamfanin amfanin gona na New Nigeria Commodity Marketing Company; da Shugaban Kungiyar Manoman Masara, Farfesoshi daga Jami’ar Ahmadu Bello (ABU).

Sauran sun hada da wani dan Majalisar Daraktoci ta Hukumar Samar da Iri ta Kasa (NASC), Ibrahim Musa; Shugaban kamfanin kayan abinci na FURSA FOOD, Alhaji Abba Dantata; da kuma hakimai da sauran masu rike da sarauta a Zariya da sauransu.

Yana da kyau a fahimci cewa abin da manoma suka fi neman bayani a kai shi ne yadda za su samu rance – a shirye muke mu samar da kudade a bangaren noma da hakar ma’adanai.

Abu na biyu da aka fi yin tambaya a kai shi ne bangaren kasuwancin noma da noman zamani da sauransu.

 

Shin wannan shiri ya kai ga cimma manufar kafa shi ta magance wadannan matsaloli kuwa?

Tun da aka fara shirin, kullum yawan masu sauraronsa da masu neman karin bayani karuwa yake ta yi saboda damar da manoma ke ta ita ta neman karin bayani domin su yi abin da ya dace.

Samar da bayanai kawai ba tare da ba da damar aiwatarwa ba ba ta da amfani. Shi ya sa bayanan da shirin ke samarwa ke sanar da manoma tsare-tsaren bankin domin bunkasa harkokinsu.

Bayanan da muka samu sun nuna kananan manoma da kanfanonin kayan noma a Arewacin Najeiya sun fi amfana saboda daga yankin muka faro kuma adadin na ci gaba da karuwa.

‘Farmers’ Radio’ ya isa dukkanin yankunan Najeriya inda ake sanya wa a gidajen radiyo a jihohi 19 domin wayar da kai da kuma ilimatarwa a kan dabarun noma da samun rancen noma ga mazauna karkara da kuma kyautata hulda tsakanin dukkanin masu ruwa da tsaki.

Sterling Bank na ba da muhimmanci ga wasu bangarorin tattalin arziki. ‘Farmers’ Radio’ daya ne daga hanyoyin tallafin bankin ga harkar noma. A 2018 bankin ya shirya babban taron noma na Afirka.

Taron na bana wanda za a yi ta intanet zai mayar da hankali ne a kan kasuwancin noma da fasahar noma da sauyin yanayi da samar da rance mai dorewa ga mata da matasa da kanana manoma ta hanyar hadin gwiwar gwamanti da kamfanoni.

Akwai kuma tsarin dakin ciniki da ke hada masu zuba jari da masu neman rance domin bunkasa harkar noma.

 

Shin kina ganin wayar da kan manoman ya yi tasiri wajen samun karuwar amfanin da suke girbewa?

Manoma sun fahimci nagartattun dabaru da kirkire-kirkire a fannin noma da suka kai ga samun karuwan amfanin da suke girbewa.

Daga ciki akwai shirin SABEX na cinikin kayan gona da ya mayar da hanakali kan adana amfanin da aka girbe da rage asarar da kuma nagartattun hanyoyin kaiwa ga kasuwanni a farashi mai daraja.

 

Daga abin da kuka gano zuwa yanzu, mene ne matsalolin kananan manoma da kuma yadda za a magance su?

 

Ta yaya kananan manoma za su bunkasa harkarsu ta yadda za a samu wadataccen abinci a cikin gida?

Za su iya fadada ayyukansu idan suna samun rance da ingantattun iri da takin zamni da kayan aiki na zamani.

Idan da lafiyayyun hanyoyin kai amfanin gona kasuwa, to za mu taimaka mu hada masu bukatar kayan gonan da manoma; su kuma manoma mu ba su kwarin gwiwar nomawa da yawa ga kamfanonin da za su saya.

Idan aka rika ba wa manoma ingataccen ilimi da kwarewa za su samu ingatattun amfani da kamfanoni masu saye ke bukata.

Da haka za mu iya samun isasshen abinci a cikin gida har a fitar kasashen waje.

 

Ta yaya za a shigar da tsarin kasuwancin noma cikin tsarin cigaban tattalin arikin Najeriya?

Bangaren noma zai iya kara karfin tattalin arzikin Najeriya saboda kasuwancin noma zai kyautata hulda tsakanin masu ruwa da tsaki a bangaren.

Zai samar wa matasa da mata ayyuka, ya rage shigo da kaya daga ketare, ya samar da wadataccen abinci a cikin gida, ya kuma kara yawan kudaden shigar gwamnati.

A matsayinmu na jagora a bangare samar da rancen noma, Sterling Bank ya gamsu cewa samar da rancen noma zai magance matsalolin da aka ambata da kuma kawo cigaban tattalin arzikin kasa a kan lokaci.

Da za a samu wasu cibiyoyin kudi za su yi koyi da mu, to da za a samu gagarumar nasara.

Kazalika akwai bukatar gwamnati ta bullo da shigar da fasaha a cikin harkar noma a fanin kasar.

A Sterling Bank, baya ga ‘Farmers’ Radio’ wanda shi ne jigon wannan hira, muna ba da bashi cikin hanzari ga manoma.

Muna kuma tattaunawa da kuma kulla yarjejeniya da gwamnati da kamfanoni da kuma hukumomin cikin gida da kasashen duniya domin kyatuta halin da ake ciki.