✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Su Obasanjo suka jefa Najeriya cikin tasku —Akinyemi

Farfesa Akinyemi ya ce su Obasanjo ne suka jefa Najeriya cikin taskun da take ciki a yanzu, don haka ya ja bankinsa ya yi shiru

Tsohon Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Farfesa Bolaji Akinyemi, ya soki tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, kan kiran da yi cewa ’yan Najeriya su zabi Peter Obi, dan takarar Jam’iyyar LP, a zaben shugaban kasa na 2023.

Farfesa Akinyemi ya ce Obasanjo na daga cikin wadanda suka jefa Najeriya a cikin mawuyacin halin da take ciki a yanzu, don haka ba shi da bakin magana ballantana ya ce wa ’yan kasar ga wanda za su zaba.

Ya yi wa Obasanjo tatas da cewa, “Ba zai yiwu ka jefa mu cikin matsala ba, sannan ka dawo daga baya kana nuna mana cewa kai ka san maganin, ai ba za mu yarda ba.”

Akinyemi ya yi wankin babban bargon ne sa’o’i bayan tsohon shugaban kasar a cikin sakonsa na taya ’yan Najeriya murnar shiga Sabuwar Shekarar 2023, ya shawarce su da su kada wa Peter Obi kuri’a a zaben shugaban kasa.

A cikin sakon, Obasanjo ya bayyana Obi a matsayin mafi nagarta ta bangaren dabi’u, ilimi, kwarewa da kuma kawo cigaba, fiye da sauran ’yan takarar shugaban kasa a zaben na ranar 25 ga Fabrairu.

Amma Farfesa Akinyemi ya ce, a matsayin Obasanjo na daya daga cikin mutanen da suka jefa Najeriya cikin taskun da take ciki a yanzu, abin da ya fi dacewa shi ne ya ja bankinsa ya yi shiru, kamar sauran tsoffin shugabannin kasar da suka koma gefe ba sa yin shisshigi a harkokin siyasa bayan sun bar mulki.

Ya ce, “Kar mu bata lokacin wannan shirin a kan wasikar Janar Obasanjo ko tunaninsa, saboda wasunmu sun yi amanna cewa yana cikin wadanda suka kawo matsalolin da kasar nan ke ciki a yanzu.

“Abin da nake nufi shi ne idan mutum ya ya shugabancin kasar nan har ya kammala wa’adinsa biyu, to ya koma gefe kamar yadda Janar [Yakubu] Gowon ya yi, ya zama irin su Janar Abdulsalami [Abubakar]… ya ja kinsa ya yi shiru kamar sauran.