✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sule Lamido da Saraki sun yi ganawar sirri da Obasanjo

Tsoffin gwamnonin PDP sun zauna da shi bayan ganawa da Abdussalam da Sarkin Musulmi.

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido tare da tsohon Gwamnan Jihar Kwara, Sanata Bukola Saraki, sun yi ganawar sirri da tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo.

Obasanjo ya karbi bakuncin tsoffin gwamnonin na jam’iyyar PDP ne ranar Juma’a a Abuja, inda suka yi wata ganawar sirri.

Sauran tsofin gwamnonin na PDP da suka yi ganawar sirrin da tsohon Shugaban Kasar sun hada da Ibrahim Hassan Dankwambo na Jihar Gombe da kuma Peter Obi da Liyel Imoke.

Kafin su ziyarci Obasanjo, tsoffin gwamnonin sun yi wata ganawar sirri da tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja, Abdulsalami Abubakar da kuma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III da wasu manyan mutane.

Hotuna: Mansur Ahmed.