✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sun farke cikin mai juna biyu sun sace jaririn cikinta a Mexico

Ana zargin takaicin rashin haihuwa ya sa maharan suka kashe matar, suka farke cikin da take dauke da shi sannan suka sace jaririn.

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne a kasar Mexico, sun farke cikin wata mata mai juna biyu sannan suka sace dan tayin da take dauke da shi.

Hukumomin kasar sun ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin, amma an samu ceto jaririn da ransa.

Rahotanni daga yankin sun ce an sace matar ce a yankin Veracruz inda suka farka cikinta suka cire dan sannan suka yar da gangar jikinta a yankin Medellin del Bravo.

Sai dai ’yan sandan yankin sun kama wadanda ake zargin; mace da namiji, bayan da aka gano suna dauke da jaririn da ba a yarda da shi ba.

’Yan sandan sun yi zargin takaicin rashin haihuwa ga matar da ake zargi da hannu a aika-aikar ya sa suka kama marigayiyar suka farke cikinta suka cire dan suka tafi da shi.

Jami’an tsaron sun ce suna ci gaba da zurfafa bincike, kuma za su bayyana sakamakon bayan kammalawa.