✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sun gina gida a Abuja ta hanyar amfani da mara lafiya wajen yin bara

Tuni dai an biya wa matar kudin tiyatar

An kama wasu mutum biyu da suka yi amfani da wata budurwa mai suna Beatrice Adah mai shekara 23 da ke fama da cutar kansa har suka tara kudin da suka gina gida a Abuja.

Mukaddashin Darakta a Sakatariyar kula da Zamantakewa ta Hukumar Birnin Tarayya (SDS) SDS, Alhaji Sani Amar ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja.

Ya ce tuni suka mika Beatrice  ga iyalanta bayan daukar nauyin yi mata tiyata.

Amar ya ce kafin jami’an SDS su shiga tsakani, mazan biyu na yawo da mara lafiyar suna samun kudi ta hanyar bara, kuma bayan sun kamo su sun bayyana masu cewa sun kai mara lafiyar Asibiti amma suka kasa biyan kudin yi mata tiyata.

A cewarsu, hakan ne ya sanya suka dau Kokon bara domin tara wadannan kudi.

Amar ya ci gaba da cewa, hukumar ta kai mara lafiyar Babban Asibitin Kasa da ke Abuja domin tabbatar da gaskiyar lamarin, inda aka tabbatar musu da fara biyan Naira 500,000 kafin a fara aikin.

To sai dai ya ce wadancan mutane sun tara miliyoyin Naira ne ta hanyar bara da sunanta, domin, har daya daga cikin su har ya sayi fili a daya daga cikin kauyukan Abuja.

“Na biyun kuma har ma ya fara gina filin nasa, duk da sunan tara mata kudin magani”, inji Amar.

“Bincikenmu ya nuna cewa mara lafiyar na hannunsu tun a watan Yulin 2020, har zuwa lokacin da muka kama su watanni biyu da suka gabata.

“Kuma cikin yardar Allah an gudanar da aikin cikin nasara, bayan wani mutum ya bayar da gudunmuwar Naira 350,000 sai kuma Hukumarmu ta FCTA da ta cika sauran.

“Su ma wadannan mazan da suka dinga yawon Bara da sunanta, mun sanya su fito da Naira dubu 500 muka kara mata don yin jinya. wanda jimilla ya zama Naira Miliyan 1,600 gaba daya,” inji Babban Daraktan.