✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

SWAT ta maye gurbin sashen ’yan sandan SARS

Sashen Makamai da Dabaru na Musamman (SWAT) zai maye gurbin SARS da aka rushe

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta kirkiro da sabon sashen na mu samman da zai maye gurbin sashen SARS mai yaki da ayyukan fashi da aka rushe.

Shugaban Rundunar Mohammed Adamu, ya sanar da bude Rundunar Makamai da Dabaru na Musamman (SWAT) wanda za a fara horas da jami’an da za su yi aiki a karkashinsa daga makon gobe.

Ya ce za a yi wa jami’an SWAT gwajin lafiyar jiki da na kwakwalwa baya ga horo na musamman da za a ba su a cibiyoyi daban-daban kafin su fara aiki.

Sanarwar da Kakakin Rundunar, Frank Mba ya fitar ta ce za a horas da jami’an SWAT daga rundunonin ’yan sanda da ke Kudu maso Gabas da Kudu mso Kudu a Kwalejin Dabarun Yaki da Ta’addanci da ke Nonwa-Tai, Jihar Ribas.

Wadanda suka fito daga rundunonin da ke Arewa kuma za a gudanar da nasu a Kwalejin Horas da ’Yan Sandan Kwantar da Tarzoma da ke Ende, Jihar Nasarawa.

Na yankin Kudu maso Yamma kuma a Kwalejin Horas da ’Yan Sandan Kwantar da Tarzoma da ke Ila-Orangun, Jihar Osun za a ba su horo.

Makomar jami’an SARS

Runduar ta umarci dukkannin jami’an SARS da su hallara a hedikwatarta da ke Abuja inda za a yi musu “jawabi da gwajin lafiya da na kwakwalwa”.

“Za a yi gwaje-gwajen ne gabanin a fara ba su sabon horo da sauya musu tunani kafin sauya musu wuraren aiki a rundunar”, inji Mba.

Ya ce sabon Sashen Bayar da Shawarwari da Taimako da rundunar ta kirkiro ne zai yi wa jami’an SARS gwajin da kuma kula da horaswa da sauya tunaninsu domin ayyukan na musamman.

Ya ce sabon sashen wanda ke bangaren kula da lafiya na rundunar ya kunshi masana halayyar dan Adam, masana ilimin kwakwalwa, likitoci, malaman addini, kwararru a fannin hulda da jama’a da kuma kungiyoyin kare hakki da na fararen hula.