✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta ina Arewa ta amfana da Gwamnatin Buhari?

Shugaba Muhammadu Buhari dan Arewa ne, jiharsa ta asali Katsina na fama da matsalolin tsaro.

Yanzu dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya shiga shekarar karshe na wa’adin mulkinsa na biyu na shekara takwas.

Saboda haka, za mu baje ayyukan gwamnatin a faifai domin mu duba kuma mu yi nazarin amfani ko rashinsa da gwamnatin Jam’iyyar APC ta kawo wa yankin Arewacin Najeriya.

Wadannan ayyuka kuwa za mu duba dukkan fannonin rayuwa da ci-gaba da kuma tattalin arziki.

Kasancewar Shugaba Muhammadu Buhari dan Arewa da ya zama Shugaban Kasa a zaben 2015, abu ne da mutane da yawa ciki da wajen Najeriya suka yi murna da kuma farin ciki da shi, kuma ko babu komai abu ne da a lokacin Arewa za ta iya bugun gaba da shi cewa danta shi ne ke jagorantar wannan kasa da ta hada mutanen Kudu da Arewa masu bambance-bambance da dama.

A wannan gwamnatin an yi ayyuka da dama na gina kasa da kuma ci gabanta kamar yadda kowace gwamnati da ta gabata ta yi.

Don haka, idan ana maganar manya-manyan ayyukan raya kasa a wannan gwamnati to galibi batu ake na gina katafariyar gadar nan da ake kira Second Niger Bridge sannan manyan ayyuka irinsu aikin gina babbar hanyar Legas zuwa Ibadan ko gina layin dogo daga Legas zuwa Fatakwal da kuma gina sabon titin jirgin kasa wanda ya hada Jihar Legas da birnin Ibadan, wadanda aka yi wa manya- manyan tashoshi na alfarma da babu irinsu a Najeriya.

Sauran manyan ayyukan hanyoyi a Kudu sun hada da filin jirgin sama da gabar teku. Wadannan manyan ayyuka ne da yankin Kudu ya ci moriyarsu karkashin wannan gwamnati ta Shugaba Muhammadu Buhari dan Arewa.

Sai dai an ce aikin gina layin dogo da ya hada Legas da Ibadan, aiki ne da zai zo har Kano, wanda a zahirin gaskiya Allah ne kadai Ya san ranar da wannan aiki zai karaso Kano, domin ko da a ce an kara wa Shugaban Kasa wasu shekara hudu ba na zaton aikin zai iso Kano.

Su dai yankin Kudu maso Yamma ko yanzu kasuwa ta watse to ba shakka dan koli ya ci riba, domin kuwa an hade Jihar Legas da birnin Ibadan a jirgin kasa bugu-da-kari kuma ga sabuwar hanyar mota da aka gwangwaje su da ita duk karkashin wannan gwamnati.

Daga cikin manyan ayyukan wannan gwamnati, har da aikin hanyar da aka bayar daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano.

Kowa ya san irin muhimmancin da wannan hanya take da shi ga mutanan Arewa, domin kuwa ita ce hanyar da ta hada Arewa maso Yamma da Babban Birnin Tarayya, Abuja, kusan in ban da a wannan lokaci aikin na matukar tafiyar hawainiya, da a ce yadda aka gaggauta yin aikin hanyar Legas zuwa Ibadan haka aka gaggauta wannan aikin hanyar to ba shakka da yanzu abin da ya rage bai wuce karashe ba.

Amma dai duk da haka muna murna da farin ciki da wannan aiki, domin ko babu komai duk wanda ya bi hanyar ya san ana aiki mai kyau da nagarta. Amma tafiyar hawainiyar da aikin yake yi ta yi yawa.

Idan muka duba aikin gina sababbin filayen jiragen sama da aka yi a Legas da Kano da Fatakwal, aiki ne mai kyau kwarai da gaske wadanda suka dace da zamani.

Amma dai mun san da cewa aiki ne da aka faro shi tun zamanin Gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Jonathan, wanda ko kafin ya sauka an ci karfin aikin, mun ji dadi da wannan gwamnati ta ci gaba da aikin ba ta tsaya ba.

Amma kowa ya ga filin jirgin saman Kano ya san ya zama kamar na Kwango Kinshasa.

Abubuwa da dama sun lalace an daina yayin galibin abubuwan da suke filin jirgin saman, kuma wannan filin jirgin sama wanda har yanzu da shi ake aiki kafin fara amfani da sabon, inda yake zama wani tushe na bunkasar tattalin arzikin Arewa.

Ba mu da tashar jirgin ruwa irin Legas bare mu samu saukin harkokin fito na harkar kasuwanci, don haka abubuwa da yawa suka tsananta a harkar kasuwanci.

Haka kuma, an soma aikin tashar tsandauri a Kano da Kaduna wadda aka fi sani da Inland Dry Port, su ma wadannan ayyukan yunkuri ne na gwamnatocin Kano da kuma Kaduna.

Aikin da in an gama shi kai-tsaye za a iya kawo kwantaina daga Hamburg a kasar Jamus zuwa birnin Kano. Aikin da ya fi kowane muhimmanci shi ne aikin gina sabuwar tashar wutar lantarki ta Mambila.

Wannan aiki kusan za mu iya cewa ya zama yaudara da tsakar rana, domin kuwa an sha jin Ministan Ayyuka Fashola yana cewa sauran kiris a kammala wannan gagarumin aiki na gina tsahar wutar lantarki wadda kai-tsaye Arewacin Najeriya ne zai amfana da ita dari bisa dari.

An yi ta yada wasu hotuna a kafafen sada zumunta cewa ga yadda aikin tashar wutar ke wakana, sai da aka yi sabon Ministan Wutar Lantarki Injiniya Saleh Mamman wanda dan asalin Jihar Taraba ne sannan ya fasa kwai ya ce a maganar gaskiya ko share wajen da za a yi aikin ba a yi ba. Wannan ya janyo ce-ce-ku-ce sosai a Najeriya.

Babban abin mamaki da daure kai shi ne, har aka yi ce-ce-ku-cen aka gama, gwamnati ba ta yi wani bincike ta gano su wane ne da laifin kantara wa al’ummar Najeriya karya ba, balle a hukunta su, haka nan wannan batu ya bi ruwa, har sai da sashin Hausa na BBC ya tura wakilinsu yankin Mambila har inda aka ce ana aikin, inda galibi mun gani daji ne mai rukuki babu abin da aka yi a wajen da yake nuna za a gudanar da aikin gina sabuwar tashar wutar lantarkin.

A hakikanin gaskiya duk wani aiki da shugaba Buhari zai yi a wannan mulkin nasa bai kai aikin wutar muhimmanci ba, domin ta sanadiyarsa masana’antu da yawa za su bubbude, dubban matasa za su samu aikin yi, amma yanzu Arewa ta yi asarar rashin yin wannan aiki.

Mutane a kauyukan Zamfara da Katsina jihar Buhari ta asali, suna cikin firgice, sun fita daga hayyacinsu, sun hakura da gidajensu da makarantunsu da sana’o’insu sun koma batun abin da za su ci sannan su kwanta su yi barci. Duk wadannan ayyukan ci-gaba ko gina kasa wannan yanki bai san shi ba.

Kuma ni tunda aka fara wannan gwamnatin ban san wani katafaren aiki da gwamnati ta aiwatar a jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara ba, babu hanya mai kyau babu tsaro, noman da yankin ya shahara da shi yanzu ya zama tarihi, kadan ne suke iya fitowa su yi noma saboda gudun abin da zai biyo baya.

Shugaba Muhammadu Buhari dan Arewa ne, jiharsa ta asali Katsina na fama da matsalolin tsaro da sace mutane a yi garkuwa da su a karbi kudin fansa, ko a tayar da kauye ko wadansu ’yan iska su shiga kauye su sanya wa mutane haraji kuma su biya, tamkar babu gwamnati a yankin.

Shugaba Buhari ya kasa warware wannan matsala, sai Asiwaju Bola Tinubu muke jira idan ya zama Shugaban Kasa ya warware matsalar tsaron da ta addabi jihohin Katsina da Zamfara?

Mai hankali yi tunani. Akwai abin da Hausawa ke cewa hannu ya san na gida, tsarin mulki bai hana Shugaban Kasa ya yi wani abu na kyautata wa mutanen yankinsa ko jiharsa ba musamman a lokacin da take cikin matsalar tsaro, amma bai yi haka ba. Da ya yi haka watakila da mun ci gajiyar wannan zango na wannan gwamnati.

Mataki-na-gaba da ake ambato, mu gan shi a zahiri ba a kan takardu ba, cewa za a gina jami’a a Daura ko za a yi titin jirgin kasa a Daura.

Kusan yanzu dukkan kwanakin da suka wuce, Shugaban Kasa ba zai sake maimaita irinsu nan gaba ba a shekara mai zuwa, face an yi sabon zabe sabon Shugaban Kasa ya hau kan karagar mulki.

Shin a wannan kwanakin ko watanni da suka rage wa Shugaban Kasa akwai wani abu da zai iya yi na taimakon Arewa?