✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta kashe Naira miliyan 62 don gina gadar sama da danta zai je makaranta

Zan yi wa gadar lakabi da suna gadar hikima saboda Daliban da suke bi ta kanta su zama masu hikima sosai.

Wata mata a Lardin Henan da ke kasar China, ta kashe sama da Dalar Amurka dubu 154 (kimanin Naira miliyan 62) wajen gina wasu gadoji saboda danta ya rika bi yana zuwa makaranta.

Matar ta gina gadojin bi-da-kafa guda biyu a kusa da makarantar da danta yake, don tabbatar da cewa shi da sauran dalibai sun ketara hanya cikin natsuwa da kwanciyar hankali.

Matar mai suna Meng ta bayyana wa gidan talabijin na Hanan TV cewa, hanyar da danta yake wucewa cike take da cinkoson ababen hawa musamman idan an kawo yara ko aka zo daukarsu.

Haka kuma, ta ce babu na’urar da za ta taimaka wajen bai wa ababen hawa hannu da daliban ke bi, ta kasance mai matukar hadari ga dalibai da malaman makarantar.

Wani dalilin da ya sa Meng ta kashe kudin aljihunta don gina gadar tsallaka hanyar ga makaranta da take kusa da hanyar, ketare hanyar na sa danta ya dawo gida kafarsa jike da ruwa.

Meng, ta ce: “Akwai wani ruwa mai zurfi a kusa da makarantar, kuma abu ne mai wahala ketare hanyar.

“Ruwa kan zauna a matakalar hanyar shiga makarantar, inda dalibai ke rabewa suna jiran iyayensu su zo su dauke su, kamar wadansu tsintsaye. Suna zama cikin zullumi.

“Kafafun dana sun canja zuwa farare saboda shiga cikin ruwa da yake yi,” inji ta.

Gadojin biyu da Meng ta fara, a yanzu haka an kusa kammala guda daga ciki yayin da dayan aka fara gina ta, kuma hakan ya samu amincewar Hukumar Kula da Gine-gine da Bunkasa Birane da Karkara, amma sun fara aikin ne ta hanyar wacce ta dauki nauyin gina gadojin biyu.

Meng ta ce, ba ta taba fada wa danta cewa ta biya kudin gina sababbin gadojin biyu ba, saboda ba ta son ya yi wa sauran daliban alfahari.

Fatar Meng shi ne taimakon da zai inganta ilimin yaran su samu ilimi.

“Na yi kawai abin da zan iya yi ne don mutum ba zai mutu ya tafi da kudi ba, sannan ba na bukatar tara kudi ga dana ya gada.

“Zan yi wa gadar lakabi da suna gadar hikima saboda Daliban da suke bi ta kanta su zama masu hikima sosai,” inji ta.