✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta kashe saurayinta kan yunkurin zubar da cikin da ya mata

Ana zargin wata mata mai shekaru 25 da yi wa saurayinta kisan gilla ta hanyar taba masa wuka a kirji saboda takaddamar da ta faru…

Ana zargin wata mata mai shekaru 25 da yi wa saurayinta kisan gilla ta hanyar taba masa wuka a kirji saboda takaddamar da ta faru a tsakaninsu.

Marigayin Eleyi Azubuike mai shekaru 29 ya gamu da ajalinsa a hannun budurwar tasa ce bayan da ya nemi a zubar da cikin da yayi mata, amma ta ki amincewa, ta kuma nemi ya dinga ba ta kudin kula da kanta da cikin har ta haife shi.

Rikici ya barke tsakanin masoyan biyu ne a ranar Laraba 2 ga watan Satumba, a gidan saurayin da ke unguwar Ochiagha a Karamar Hukumar  Idemili ta Arewa a Jihar Anambara, inda wacce ake zargin ta daba wa saurayin wuka a kirji.

Da ’yan sanda suka ziyarci gidan sun iske saurayin  cikin jini a mawuyacin hali, kuma nan take kuma aka garzaya da shi asibiti amma likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra SP  Haruna Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce an kai gawar saurayin dakin ajiyar gawa domin bincike.

“Binciken da muka fara mun gano sukar da aka yi da wuka a kirjin gawar, sannan mun gano wukar dakin girki dauke da jini a jikinta.

“Haka mun gano cewa ya yi wa wacce ake zargin ciki ne, kuma ya bukaci zubar da cikin.

“Rikici ya barke a tsakaninsu bayan da ta nemi ya dinga ba ta kudin da zata kula da kanta, amma yaki yin hakan, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa”, inji SP Muhammad.

Ya ce an kame wacce ake zargin, ana kuma ci gaba da binciken lamarin.