✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta rayu shekara 20 da almakashi 2 da likitoci suka manta a cinkinta

An dai manta da almakashin a cikin nata ne tun a 2002.

Wata mata ’yar kasar Bangladesh wadda ta dade tana fama da ciwon ciki a tsawon shekara 20 a-kai-a-kai, ta firgita bayan an gano cewa, tana rayuwa ne da wasu almakashi biyu da aka manta a cikinta bayan an yi mata tiyata.

Matar mai suna Bachena Khatun, mai shekara 55, ta yi ta fama da ciwon ciki a-kai-a-kai bayan yi mata tiyatar cire tsakuwa a wani asibiti da ke Chuadanga a shekarar 2002. Bayan tiyatar, an sallame ta daga asibitin tare da rubuta mata magani.

Amma bayan kwanaki kadan ta fara jin zafi a cikinta. Sai ta koma asibitin, amma wani likitan fida da ya duba ta da wasu likitoci biyu da suke kula da su yayin aikin, ya yi watsi da matsalrta yana cewa ciwon ba wani abin damuwa ba ne ta kwantar da hankalinta.

Ya yi kuskure, kuma ba shi kadai ba ne ke yin hakan.Ya nuna mata ciwon ciki bai dawwama, sai Bachena ta bar likitan zuwa wajen wani, inda ta ce tun bayan yi mata tiyata tana yawan jin ciwo a-kai-a-kai, amma abin da take kawai shi ne shan magunguna don rage radadin ciwon.

A tsawon shekarun, an tilasta wa matar sayar da shanu biyu da kadarorinta, don biyan kudin magungunan da fatar za a magance ciwon.

Abin takaici, duk kokarin Bachena ya zamo na banza, domin ciwon cikin ya tsananta ta yadda ba za ta iya jurewa ba.

A wannan karo, bisa shawarar likita a karshe aka dauki hoton ciki, inda aka gano almakashi biyu da aka manta a cikinta, bayan an yi mata tiyatar farko shekara 20 da suka wuce.

A makon jiya ne, Bachena Khatun ta kwanta a asibitin Chuadanga Sadar, inda likitoci suka yi kokarin bincike don gano ko tana da ciwon sukari, kuma ana cikin binciken ne aka gano almakashin biyu, aka cire su cikin sauki, bayan yi mata tiyata, yanzu haka dai tana samun sauki.

Likitan tiyatar, Dokta Jawaherul Islam ya ce, an kafa wani kwamiti mai mutum uku da zai binciki yadda almakashin biyu suka kasance a cikin Bachena na tsawon lokaci.

Aukuwar irin wadannan abubuwa ne da ake samu jefi-jefi inda a shekarar 2019, muka ba da rahoton wata mata ’yar kasar Rasha da aka yi mata tiyata a shekara 23 da suka gabata aka manta da alkamakashi a cikinta.