✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta sake Musulunta bayan shekara 36 da komawa bautar dodo

Malama Tawakat Tonwe, dattijuwa ce mai shekara 84 a duniya da ta fito daga kabilar Cakiri (Itsekiri), wadda ta taba shiga addinin Musulunci, amma daga…

Malama Tawakat Tonwe, dattijuwa ce mai shekara 84 a duniya da ta fito daga kabilar Cakiri (Itsekiri), wadda ta taba shiga addinin Musulunci, amma daga baya ta sake komawa addinin gargajiya, sai dai a ranar Asabar din makon jiya ta sake dawowa cikin addinin Musulunci a garin Warri da ke Jihar Delta.

Daya daga cikin ’ya’yan dattijuwar mai suna Imam Sadik Oniyesaneyane Musa mai shekara 49 wanda Babban Kwamishina ne a Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON) mai wakiltar Kudu maso Kudu, kuma malami mai da’awa da ke da wata kungiya mai suna Imam Musa Multimedia ne ya shaida wa Aminiya haka.

Bayanin dan Malama Tawakat Tonwe

Imam Musa, ya ce mahaifiyarsa Malama Tawakat Tonye, ta auri wadansu mutum biyu ta haifi ’ya’ya uku da mijinta na farko ta haifi ’ya mace a aurenta na biyu sannan mahaifinsa ya aure ta, ta haifi su biyar.

Ya ce mahaifiyarsu ta kai shekara 84 a duniya. “Mahaifina shi ne limamin garin Warri na farko. Kuma Musulunci ya shiga yankin Neja-Delta ne daga yankin Kogi da Edo tun 1890 ta hannun ’yan kasuwa.

Mu Musulmi a Warri ta Jihar Delta ba mu wuce dubu daya ba. Bayan da mahaifina ya aure ta. Sai ya musuluntar da ita daga addinin gargajiya mai suna Rikomo.

Bayan ta haife mu mu biyar, Ina da shekara 11, sai aka kai ni garin Edo makarantar Islamiyya, kafin in dawo sun rabu, kuma ta koma addinin gargajiya. Kada ka tambaye ni dalilin, don ba ta taba gaya min ba, ni kuma ban taba tambayar ba,” inji shi.

Imam Musa ya ce akasarin mutanensu suna bin addinin Kirista ne da addinin gagajiya sai Musulmi kalilan, sai dai ya ce masu bin addninn gargajiyar ba su bayyana addininsu sai dai su nuna su Kirista ne, su yi rufa- rufa.

Imam Musa, ya ce, mahaifiyarsu ta kwashe shekara 36 da komawa bautar dodo. ”Ni kuma ga shi ina wa’azi, ina kawo masu wa’azi, ina cikin jagorori masu kula da aikin Hajji, sai na lura cewa zamani ya sa ana gudunta don tsufa da camfi.”

Sai na yi wuf na rika kyautata mata ina yi mata wa’azi cewa Musulunci ya yi horo a kyautata wa iyaye da yi musu gata ba a kyamace su ba.

Wannan hali na kwarai ya sa na jawo hankalinta har ta sake rungumar Musulunci ranar Asabar din makon jiya,” inji shi

Imam Musa ya ce Musulmi suna samun tsangwama kadan, inda a wasu lokuta ake ce musu masu bin addinin Hausawa. “Amma babban abin murna shi ne ba a taba samun rikicin addini ba a yankin Neja-Delta.

Dalili shi ne ba a kyamar mutum don yana bin addinin Musulunci ko Kiritsa ko gargajiya. Mu a gidanmu akwai Musulmi da Kirista.

A wasu gidajen akwai masu yin addinan nan uku kuma suna zaune lafiya. An gina masallaci na farko a garin Warri a 1892, Olu na Warri na yanzu Kirista ne, amma kanensa Musulmi ne, shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Jihar Delta ka ga dan sarkin Musulmi ne,” inji shi.

Kan ko sauran ’ya’yan mhaifiyarsu Tawakat Tomwe, Kirista sun nuna bacin ransu da wannan hobbasa da ya yi?

Sai Imam Musa ya ce wadanda suka yi watsi da ita, me za su ce? Ai ba ta rude ba, tana da hankali da natsuwa da lafiya, ita da kanta ta karbi kalmar shahada.

“Ban taba jin dadi kamar wannan Asabar da ta wuce ba, don ina wa’azi, na taba musuluntar da mutum 364 a yankinmu, na ji dadi amma sake karbar kalmar shahadar da mahaifiyata ta yi, ya fi min dadi. Ina kira ga Musulmi su rika nuna hali na kwari don ta haka aka fi jan mutane su musulunta fiye da yin wa’azi,” inji shi.