✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta sanya kawayenta shirya mata jana’izar karya

Ta bayyana cewa tabbatar wannan rana mafarkinta ya cika.

Wata mata mai suna Mayra Alonzo mai shekara 59, daga Jamhuriyar Dominika, ta shirya jana’izarta ta karya a garin Santiago.

Matar ta yi ado daga kanta har zuwa yatsunta da fararen kaya, tare da toshe hancinta don a zaci gawar gaske ce.

Abin ban mamaki game da Mayra, shi ne danginta da abokan arziki sun amince da shirinta.

’Yan uwanta sun ba ta hadin kai ta hanyar zagaye akwatun gawar suna kuka da zubar da hawaye na karya kuma suna ban-kwana da Mayra, sai dai hakan a zahiri ba gaske ba ne.

Dukkansu sun zauna suna cin abinci da abin sha kuma suna tuno abubuwan da suka fi so tare da ita, yayin da take kwance a akwatun gawa tana sauraronsu.

A tunaninta hakan zai zama kyakkyawan yabo mafi girma, saboda kowa yana tofa albarkacin bakinsa kan rabuwarsu da ita.

Mayra ta kashe kusan Dalar Amurka 1,000 (daidai da Naira dubu 480) a ranar da aka shirya mutuwar karyar.

Sai dai a bayyane wannan bikin mutuwar mai sauki ne idan aka kwatanta da jana’izar yau da kullum da ake yi a kasar.

Hakan ba lallai ne ya kunshi kudin akwati da na kone gawa ko gini a kan gawar don nuna shaida ba.

Wadannan duk abubuwan da ake bukata wajen gudanar da jana’izar gaske a kasar.

Ko yaya dai, wannan rana ta zama babbar rana a wurin Mayra, wadda ta bayyana ta a matsayin “mafarkinta ya cika”.

Ta kuma bayar da kyautar ’yan lu’u lu’u ta hanyar hikima ga wadanda suka nuna kaunarta a yayin jana’izar karyar da ta shirya.