✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta tabbata Cristiano Ronaldo ya bar Juventus

Dan wasan ya sanarwa da kungiyar ra'ayinsa na son sauya sheka.

Fitaccen dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Cristiano Ronaldo ya bar ta bayan shafe shekara uku yana murza mata leda.

Kocin Juventus, Massimilano Allegri, ya tabbatar a ranar Juma’a cewa dan wasan ba zai ci gaba da zama a kungiyar ba.

Tuni wakilin dan wasan Jorge Mendes ya shiga neman kulla yarjejeniya tsakanin Ronaldo da kungiyar Manchester City.

Sai dai tsohuwar kungiyar dan wasan, Manchester United ta hannun kocinta Solskjaer, ta tabbatar da cewar tana sha’awar sake daukar dan wasan.

A yanzu dai Wakilin Ronaldo, Jorge Mendes, na ci gaba da tattaunawa da kungiyoyin biyu, don ganin inda dan wasan ya fi dacewa ya koma da murza leda.