✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta taimaka wa mijinta auren tsohuwar budurwarsa

Nitya da Bimala sun amince za su zauna gida.

Wata Ba’indiyiya ta gano cewa, har yanzu mijinta da tsohuwar budurwarsa suna son junansu, sai ta amince da tsohuwar budurwar ta zo su zauna tare a matsayin kishiyarta.

Wannan labarin soyayya mai ban mamaki ya faru ne a garin Tirupatida ke Jihar Andhra Pradesh ta Indiya.

Kalyan dai ya kasance mai sana’ar yin bidiyo a cikin gida, inda yake auren wata mata mai suna Vimala.

Suna cikin rayuwar aurensu ne Vimala ta samu labarin cewa, mijinta yana soyayya da tsohuwar budurwarsa ‘yar garin Visakhapatnam wadda ta yi kaura zuwa yankinsu kuma tana daf da auren sa.

Maimakon ta yi kokarin ruguza soyayyar, sai ta ba da kai bori ya hau, inda ta amince da ya auri tsohuwar budurwar tasa don ta zauna tare a matsayin kishiyoyi.

Daga dama Vimala matar Kalyan ta farko, Kalyan a tsakiya sai amaryarsa Nitya Sree

A cewar kafafen yada labarai na Indiya, Kalyan da tsohuwar budurwarsa Nitya Sree, sun rabu ne saboda wasu batutuwan da ba a bayyana ba da aka warware tun a wancan lokacin.

Lokacin da ta koma Tirupati ta sake haduwa da shi, inda suka fahimci cewa har yanzu suna son juna, don haka sai suka roki Bimala ta bar shi ya auri tsohuwar budurwarsa.

Da farko an yi zaton Vimala ta rude, amma bayan ta dauki dan lokaci tana tunani a kan batun, inda ba kawai yanke shawarar ba wa majinta goyan baya ta yi ba, har da shiga shirye-shiyen biki da kuma daukar hoto tare da angonta da kishiyarta ranar auren.

Nitya da Vimala sun amince za su zauna gida.

Labarin soyayya mai cike da abin al’ajabi ya dade yana zagayawa a shafukan sada zumunta na Indiya.

Wasu sun zargi mutumin da wulakanta matarsa ta hanyar auren tsohuwar budurwarsa a wajen ibada, yayin da wasu suka yaba wa Vimala bisa mutunta bukatun mijinta.