✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta yiwu Cristiano Ronaldo zai bar Juventus

Ga alama Juventus za ta cewa dan wasanta Ronaldo ya cika bujensa da iska.

A wani rahoto da jaridar RFI Hausa ta wallafa ya ce, kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta fara shirye-shiryen sayen Kylian Mbappe, dan wasan gaba na kungiyar Paris Saint Germain ta Faransa.

Hakan ka iya sanya Juventus ta raba gari da fitaccen dan wasanta, Cristiano Ronaldo, domin bai wa Mbappe damar watayawa, duba da yadda duniyar kwallon kafa ke yi wa dan wasan kallo a matsayin mafi daraja a yanzu haka.

Kasancewar dan wasan zai bukaci albashi mai tsoka muddin cinikin ya tabbata, ga alama Juventus za ta cewa dan wasanta Ronaldo ya cika bujensa da iska domin ba za ta iya rike su tare a lokaci guda ba wajen biyan albashinsu.

Rahotanni na hasashen cewa, cikayyar Mbappe za ta iya mamaye kasuwar musayar ‘yan wasa a kaka mai zuwa, biyo bayan sanarwar da dan wasan ya yi wa kungiyarsa ta cewa yana sha’awar sauya sheka.

Kazalika muddin cinikayyar ta tabbatar, matakin zai zama koma baya ga kungiyar Real Madrid da Livervool a yayin da ba a bar su a baya ba wajen hankoron sayen dan wasan.