✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ta’addanci: Halin da ake ciki bayan kama ‘dan uwan’ Bafarawa

An kama dan ’yar uwar Bafarawa kan alaka da Bello Turji, ana kuma dambarwa kan alakar dan cikinsa da ’yan bindiga

Jami’an tsaro sun kama Musa Kamarawa, dan ’yar uwar tsohon Jihar Sakkwato, Attahihu Bafarawa, kan alakarsa da jagoran ’yan bindiga, Bello Turji.

Wata dambarwa kuma ta kunno kai cewa binciken Musa Kamarawa ya kai ga jami’an tsaro sun tsare dan cikin tsohon gwamnan, wato Sagir Attahiru Bafarawa — wanda shi ne Kwamishinan Muhalli na Jihar Sakkwato.

Matsalar tabarbarewar tsaro ta ta’azzara a Gabashin Sakkwato, inda kusan kullum sai an kai hari a yankin da ’yan bindiga ke cin karensu babu babbaka.

Ta kai ga a baya an yi fama da tashin hankali da salwatar rayuwar mutanen yankin, an hana su noma da kiwo, wanda su kadai ne suka dogara da su.

Matsalar ta haifar da ’yan gudun hijira da zawarawa da marayu masu tarin yawa, abin da ya kai ga duk wanda ba a yankin yake ba ya daina zuwa, duk wani da yake da wata madafa ya bar yankin tare da iyalansa domin tseratar da rayuwarsa da iyalansa.

Ana cikin haka sai labari ya watsu cewa jami’an tsaro sun kama Musa Kamarawa, bayan nan sai ga bidiyo inda Musa yake bayanin dangantakarsa da jagoran ’yan bindigar nan Bello Turji wanda ya ce amininsa ne.

Musa Kamarawa dan shekara 33, an haife shi a garin Kamarawa Karamar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato.

A bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta, ’yan sanda ne ke yi masa tambaya, yana amsa dangane da zargin da ake yi masa na mu’amala da miyagun makamai da hulda da ’yan bindiga da sayo makamai yana sayar musu.

Ya yi bayanin cewa mahaifiyarsa ita ce yayar tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa.

A cewar Musa Kamarawa: “Turji babban dan ta’adda ne da ke dajin Kagara har zuwa Fakai.

“Ya shahara wurin garkuwa da mutane da kisan mutane da satar shanu a Arewacin Najeriya.

“Shi aminina ne. Yana kira na ina kiransa, babban aminina ne.

“In sun yi garkuwa da mutane suna kai su daji, inda gidajensu suke sai an biya kudin fansa.

“Suna rike manyan bindigogi na AK 47 da wadda ake daurawa a mota da wata kundu da ake harbin jirgi da ita, dukkansu suna rikewa.”

Daga bayyanar wannan ne sai abubuwa suka sauya a yankin, kamar yadda mutanen yankin ke fadi.

“A Gaskiya tun bayan kama Musa abubuwa sun sauya a yankin namu, domin ’yan bindigar sun rage kai mana hari duk da suna shigowa amma ba kamar a baya ba.

Shekaran jiya ma sun tafi Lugu, har dayan ya kashe dan uwansa.

A baya da suke zuwa su tayar da gari gaba daya amma yanzu mun yi kusan wata daya ba wani gari da aka tayar.

Sai dai shigar sunkuru da suke yi, domin har yanzu suna nan cikin dajin da suke zaune,” a cewar majiyar.

Ya ce kamen Kamarawa ne ya sanya Turji ya rubuta takardar neman sulhu, domin wanda yake idonsa yana hannu. Hakan ya sa ya sauya wurin fakewa don bai san shirin jami’an tsaro ba.

A wannan makon sai ga wani bayani ya fito, cewa jami’an tsaro sun kama dan tsohon Gwamnan Sakkwato, Sagir Attahiru Dalhatu Bafarawa kan binciken da ake yi wa dan uwansa Musa Kamarawa.

Sai dai kuma ya musanta cewa jami’an tsaro sun kama shi. Sagir ya ce labarin an shirya shi ne domin a bata masa suna. “Ba wani kama ni da aka yi kan wai ina tare da ’yan bindiga.

“Ka gan ni yanzu ina tare da iyalina cikin kwanciyar hankali ina harkokina na yau da kullum.

“Labaran da ake yadawa domin a bata min suna ne da wasu makiya ke yi.

“Kan haka nake kira ga mutanen Sakkwato da Najeriya su yi watsi da wannan labari na karya da wasu bata gari suka shirya,” a cewarsa.

A bayanin da makusancinsa Alhaji Abubakar Sambo ya bai wa manema labarai, ya ce Sagir wanda Kwamishina ne a Ma’aikatar Kula da Muhalli ta Jihar Sakkwato, ya shawarci jami’an tsaro da su binciki lamarin don hukunta wadanda suka bayar da labarin na karya.

Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Sabon Birni, Idris Muhammad Gobir, ya nuna cewa har yanzu yankin na fama da matsalar tsaro.

A cewarsa, “Halin da yankin Sakkwato ta Gabas yake ciki babu dadi, duk da cewa a wurin baki, wadanda ba yankin suke ba za su ga ya ragu, amma mu ’yan gida da muka san inda mutanenmu suke da halin da suke ciki mun san ba dadi.

“A duk garin da yake yankin Sabon Birni da suka gudu daga garinsu, ba wanda ya dawo har yanzu da nake magana da kai.

“A wannan rana ta Talata ta wannan makon, sai da mutane suka baro garinsu da maraice ma na hadu da mutane suna barin garuruwansu a tsakanin iyakarmu da Karamar Hukumar Goronyo.”