✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’addanci: Kungiyar Ansaru ta fara daukar mayaka a Kaduna

Wasu mazauna yankunan da ’yan bindiga suka addaba na ganin mayakan Ansaru a matsayin masu kare su

Kungiyar ta’addanci ta Ansaru ta fara gangamin daukar mayaka a yankin Karamar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.

Kungiyar ta Ansaru, wadda tun da farko ta balle daga Boko Haram, ta dade tana kai komo a yankin na Birnin Gwari, inda ya jima yana fama da hare-haren ’yan bindiga.

Aminiya ta gano cewa a ranar Laraba ne dandazon ’yan kungiyar suka yi cikar kwari a kauyukan Damari da Farin Ruwa da Kwasa Kwasa da Kuyello da Gobirawa da Tabanni da Kutemeshi da kuma Kazage domin daukar mayaka.

Mayakan na Ansaru sun shiga yankunan ne da sunan taya mazauna gudananar da shagulgulan Karamar Sallah, inda suka rika wasa da babura suna raba Barka da Sallah da kuma takardu da kasa-kasai da sauran abubuwan wayar da kai kan ayyukan kungiyar.

Karamar Hukumar Birnin Gwari da ke yankin Kaduna ta Tsakiya ta dade tana fama da ayyukan ’yan bindiga, matsalar da ta fi muni a Kudanci da kuma Gabashin yankin.

A watan Oktoban 2021, Aminiya ta kawo rahoton yadda wani kazamin fada ya barke tsakanin mayakan Ansaru da ’yan bindiga a yankin, inda mayakan suka kashe ’yan bindiga akalla 30 a kusa da kauyen Damari a karamar hukumar.

Majiyoyi masu tushe sun tabbatar wa wakilinmu cewa fadan da aka shafe mako uku ana gwabzawa ya samo asali ne daga rikicin nuna karfin iko tsakanin ’yan Ansaru da bangaren ’yan bindiga a yankin.

Majiyoyin sun ce, rikicin ya barke ne bayan ’yan Ansaru da suka gudo daga Jihar Zamfara, sakamakon fatattakar su da sojoji suka yi, sun sauka a kauyukan Saulawa da kuma Damari, har suka kafa tutarsu.

Ranar 5 ga watan Afrilu, wasu mahara da ake kyautata zaton ’yan Ansaru ne sun kai wa wani karamin sansanin soja a hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna hari, suka kashe soja 11 da fararen hula hudu, suka kona motar yakin sojojin, bayan wadanda suka jikkata.

Mun tuntubi Kwamisihinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, wanda ya tabbatar cewa Gwamantin Jihar Kaduna ta samu bayanan sirri kan barazanar ta Ansaru kuma ta sanar da hukumomin da ya dace.

Sakon Ansaru

Aminiya ta samu ganin kananan takardun da kunigiyar ta yada mai taken, ‘Ba Boko Haram Muke Ba’, Sunanmu Ansaru, wanda aka rubuta da tsarin tambaya da amsa, ya bayyana cewa “Sunan Jama’atul Ansaril Muslimina Fi Biladis Sudan.”

Takardun ne ke neman jan ra’ayin mutane su shiga kungiyar sun yi bayanin manufarta, wadda ta shi shi ne Jihadi, bisa Kura’ani da Sunna, ba tare da tsattsauran ra’ayi ba.

A cewarsu babu ruwansu da bambancin akida ko kai hare-hare a wuraren taruwar jama’a kuma babu ruwansu da neman abin duniya ko wani matsayi.

Amma masana harkar tsaro da wakilanmu suka tattauna da su sun yi watsi da ikirarin kungiyar, inda suka bayyana cewa wajibi ne gwamnati da malaman addini da sarakuna su tashi haikan domin kauce wa irin abin da ya faru na Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.

Masanan sun bayyana cewa masu tsattsauran ra’ayi sun saba yin irin wannan dadin bakin domin jan ra’ayin mutane su fada a taronsu kafin daga baya su fito da munanan akidunsu na tashin hankali da ya saba wa koyarwar addinin Musulunci.

Su ne masu cetonmu — Mazuana

Majiyoyi suns shaida wa wakilanmu cewa mayakan da suka shiga yankin a kan babura sun rika gudanar da wa’azi kan nisantar yin abubuwan da suka saba wa koyarwar addinin a lokacin bukukuwan Sallah.

Wasu mazauna kuma sun yi maraba da su a matsayin masu ba su kariya daga hare-haren ’yan bindigar da suka addabi yankin.

Wani mazaunin yankin, wanda ya tabbatar da zuwan mayakan ya ce, sun yi ta wasa da babura sannan suka yi ta raba wa mutana biskit.

“Sun je Kuyello da Tabanni da Kutemeshi da kuma kauyenmu, Kazage domin shiga wasan Sallah.

“Sun shiga an yi wasan babura da su; babu wanda aka cutar kuma sun yi wa’azi cewa banda mugun wasa, kuma sun raba biskit,” inji shi.

A cewarsa, ba su damu ba da zuwan kungiyar, domin suna kallon su a matsayin masu ba su kariya daga ’yan bindaga saboda “Da zuwansu, ’yan bindiga ba za su yi gangancin kawo wa kauyukanmu hari ba.”

Wani mazaunin Kuyello ya ce tun kafin ranar Sallah ’yan kungiyar suka raba kananan takardu taya murnar Karamar Sallah tare da kiran mutane su shiga kungiyar.

A cewarsa, ba a san kungiyar da kai hari kan mutane ba, sai dai yin wa’azi da kuma bayar da kariya ga mutan daga ’yan bindiga.

“A lokacin wa’azin sun bukaci mutane su shiga kungiyar, suna shaida mana cea su ba ’yan Boko Haram ba be,” in ji shi, yana mai cewa, ko da yake ba su shiga kwaryar garin Kuyello ba, amma sun zaga kauykan da ke zagayen.

Shi ma wani dan yankin, ya bayyana cewa matasa da dama a yankin sun bayyana sha’awarsu ta shi kungiyar domin samun kariya daga ’yan bindiga.

“Akwai wasu yankuna da ’yan Ansaru suka ba wa mazauna dama su rika zuwa gonankinsu suna kuma gadin mazauna yankunan da gonakinsu,” kamar yadda ya bayyana.

‘Sun cike gibin da gwamnati ta bari’

Wani dan banga a Damari ya ce kasancewar gwamnati ta gaza wajen kare rayukan jama’a, mutane da dama a yankin sun yanke shawarar zama mambobin kungiyar Ansaru domin samun kariya.

“Mun gaji da mgana kan abu daya, idan shgia kungiyar ce za ta ba mu kariya daga ’yan bindiga, ina ganin kawai za mu yi kundumbala,” inji shi.

Salonsu daya da na Boko Haram -Masana

Amma wani masani kan ayyukan ta’addanci a Arewacin Najeriya, Musa Bala, ya bayyana cewa abin da Ansaru ke yi a yanzu ba shi da bambanci da yadda Boko Haram ta bi wajen yaudarar ’yan Najeriya su shiga cikinta a baya.

Ya bayyana cewa matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a Najeriya musamman a yankunan karkara da ’yan bindiga suka hana zuwa gonaki da sauran harkokinsu, zai jefa mutane da dama cikin hadarin shiga Ansaru.

“Yanzu Ansaru na wa mutane wa’azi da alkawarin kare su hare-haren ’yan bindiga da cin zalin da jami’an gwamnati suka yi musu, amma duk karya ce, dabara ce kawai ta tara mabiya domin ta samu damar kai hare-hare a nan gaba,” inji shi.

Ya ce alkawarin kariyar da suke yi na wucin gadi ne, nan gaba za su kakaba wa mutanen yankunan haraji, su tilasta su yin noma a gonakin kungiyar tare da tursasa su yin abubuwa iri-iri.

“Za a yi wa ’yan mata aure dole da mambobin Ansaru, a hankali-hankali abubawan za su bayyana, amma a lokacin zai zama an riga an makara, mutane ba za su iya cewa a’a ba, domin duk wanda ya ja da su bayan sun yi karfi to ya shiga uku.

“Nan gaba in aka yi sakaci za su kafa daula inda su za su kafa dokokin yadda za a rigka gudanar da rayuwa,” inji shi.   

A cewarsa, dalilin da ’yan Ansaru ba su fara kai hari a yankin Kaduna shi ne rashin yawansu, ga shi kuma ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane sun yi kaka-gida dazukan.

“Yanzu suna kara yawa, shi ya sa suke so su mamaye ko’ina. Harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga watan Maris ya nuna irin abin da suke shiryawa kuma sun yin duk mai yiwuwa domin cin karfin jami’an tsaro.

“Ina da yakin cewa Ansaru ne ta kai wa jirgin kasan hari, duk da cewa ba a tabbatar ba. Sun yi garkuwa da mutanen ne domin a sako wadansu kwamandojojinsu da mambobi,” in ji.

Har zuwa lokacin da muka kammala hada wannan rahoto babu wata sanarwa daga Gwamnatin Jihar Kaduna ko hukumomin tsaro a kan wannan batu.

Daga Sagir Kano Saleh, Lami Sadiq, Mohammed I. Yaba, Kaduna.