✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’addanci: Pantami ya nesanta kansa da kalamansa na baya kan Al-Ka’ida da Taliban

Sai dai ya yi zargin cewa akwai siyasa a zarge-zargen dake alakanta shi da kalaman.

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Isa Ali Pantami ya nesanta kansa daga kalaman da ya taba yi a baya masu cike da cece-kuce kan kungiyoyin Al-Ka’ida da Taliban a baya.

Ministan dai a ’yan kwanakin nan ya yi ta fuskantar matsin lamba kan kalamansa a wancan lokacin wadanda wasu ke fassarawa da goyon bayan ta’addanci.

To sai dai da yake amsa tambaya yayin Tafsirin watan Ramadan da yake gudanarwa a Masallacin Juma’a na Annur dake Abuja, Pantami ya ce yanzu ya dada fahimtar kalaman da ya yi a baya.

Sai dai ya yi zargin cewa akwai siyasa a zarge-zargen dake alakanta shi da kalaman.

“Sama da shekaru 15, na zaga sassa daban-daban na Najeriya ina wa’azi domin fahimtar da jama’a kan illar ta’addanci. Na je jihohin Katsina da Gombe da Borno da Kano da Difa a Jamhuriyar Nijar.

“Na kalubalanci masu akidar Boko Haram a baya da dama. Na wallafa rubuce-rubuce da dama a harsunan Hausa da Larabci da Turanci. Kuma na sami nasarar canza tunanin wasu daga cikinsu da dama kuma sun dawo kan hanya madaidaiciya.

“Wasu daga cikin wadannan kalaman da suka tayar da kura na yi su ne a baya saboda fahimtata da al’amuran addini a wancan lokacin, yanzu kuma na canza matsayina a kan su saboda hujjoji da kuma shekaru.

“Ina da karancin shekaru a wancan lokacin, a lokacin ina jami’a ne. Na fara wa’azi tun ina shekara 13 a duniya.

“Malamai da dama ba su fahimci yadda batutuwan kasa da kasa suke ba, lamarin da yake sa su daukar irin wadannan matakan, amma daga baya idan suka fahimta su kan canza matsayinsu a kai,” inji Pantami.