✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’addanci zai iya dore wa tsawon shekaru 20 a Najeriya —Buratai

Akwai rashin fahimta game da abin da tawaye da ta’addanci suka kunsa.

Babban Hafsan Sojin Kasan Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, ya ce da yiwuwar ta’addanci ya ci gaba dore wa a kasar nan har zuwa tsawon shekaru ashirin masu zuwa.

Janar Buratai ya bayyana hakan a ranar Talata cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, kwanaki kadan bayan kisan gillar da mayakan Boko Haram suka yi wa Manoman Shinkafa a jihar Borno.

Ya wallafa cewa: “Akwai rashin fahimta game da abin da tawaye da ta’addanci suka kunsa.

“Akwai yiwuwar ta’addanci ya ci gaba da ta’azzara a Najeriya har na tsawon shekaru 20 sai dai hakan ya danganta ne kawai da matakin ci gaban ta’addanci da kuma rawar da ya dace a taka ta dukkan masu ruwa da tsaki na hukumomin farar hula da na soja.”

“Haka kuma ya danganta da rawar da masu ruwa da tsaki na cikin gida da na ketare za su taka.”

“Akwai hakkin da rataya a wuyan ’yan kasa wanda yana da matukar muhimmaci kuma ya zama wajibi su bayar da ta su gudunmuwar.”

“Wajibi ne kowa ya ba da hadin kai don shawo kan matsalar tsaro wajen yin aiki tare da sauke nauyin da rataya a kan kowa baki daya,” a cewar Buratai.

Kazalika, Rundunar Sojin Kasan Najeriya ta ayyana yau Alhamis a matsayin ranar da za ta sake gudanar da wani taro karo na biyu domin fadakarwa da kara wa juna sani kan dakile duk wata farfaganda ta kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram.

Mukaddashin Mai Magana da Yawun Rundunar Sojin, Kanal Sagir Musa ne ya bayyana hakan yayin zanta wa da Aminiya a ranar Laraba.

A shekarar da ta gabata ne Rundunar Sojin Kasan ta kaddamar da shirin a karo na farko domin gudanar da taron kara wa juna sani kan yaki da ta’addanci da duk wasu ababe na tayar da zaune tsaye.