✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’aziya: Ganduje ya kai wa Danzago ziyara har gida

Ganduje ya ce shekarar 2022 lokaci ne na yin sulhu da abokan hamayya.

A yau Lahadi ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya kai wa Alhaji Ahmadu Haruna Zago ziyara inda ya jajanta masa kan rasuwar wani yayansa, Alhaji Shuaibu Haruna Zago.

Aminiya ta samu rahoton cewa mamacin ya riga mu gidan gaskiya ne a ranar Asabar da yammaci, kuma ya yi kwanan keso aka yi jana’izarsa a safiyar ranar Lahadi kamar yadda addinin Islama ya tanadar.

Ganduje ya kai wa Danzago ziyarar ce har gidansa da ke Unguwar Kurna a Karamar Hukumar Dala, tare da tawagarsa ciki har da Abdullahi Abbas.

Abdullahi Abbas shi ne wanda tsagin Gwamna Ganduje ya rika a matsayin shugaban jam’iyyar APC na Kano, yayin da kuma tsagin tsohon gwamnan Jihar, Malam Ibrahim Shekarau ya riki Danzago a matsayin shugaban jam’iyyar.

Har kawo yanzu dai ana ci gaba da rikici a jam’iyyar APC reshen Jihar Kano, inda tun bayan gudanar da babban taronta shugabannin jam’iyyar biyu suka bulla a jihar.

Sai dai a halin yanzu karo uku ke nan da wata Babbar Kotu a Abuja ta yi watsi da korafin tsagin Gwamna Ganduje, inda kuma ta tabbatar da Danzago a matsayin amintaccen shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano da ya fito daga tsagin tsohon gwamna Shekarau.

A baya bayan nan dai Gwamna Ganduje ya rika kai wa abokan hamayyarsa na siyasa ziyara sabanin yadda aka rika gani a baya gabanin tunkarowar babban zaben kasa da zai gudana a badi.

Bayanai sun ce Ganduje ya kai irin wannan ziyara gidan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda a wurinsa ya yi gadon kujerar da yake kai a yanzu amma daga bisani gaba irin ta siyasa ta shiga tsakaninsu.

Ana iya tuna cewa, a jawabin da Ganduje ya yi a ranar karshe ta shekarar 2021, ya zayyana cewa shekarar 2022 da za ta kama, shekara ce ta yin sulhu da duk wadanda ba sa  yar ga maciji a tsakinsu.