✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’aziyyar Hanifa da Ahmad Bamba ta kai Aisha Buhari Kano

Muna addu’a kuma muna fatan za a yi mata adalci.

Uwar gidan shugaban Kasa, Aisha Buhari, ta kai ziyara Jihar Kano domin jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar kan mutuwar Hanifa Abubakar da kuma rasuwar fitaccen Malami, Dokta Ahmad Bamba.

A jawabin da ta yi wa manema labarai a Fadar Gwamnatin Kano, uwar gidan shugaban kasar ta ce ta kawo ziyara ne a domin ta yi ta’aziyya ga iyalan mamatan biyu.

A cewarta, “Na kawo ziyara nan Jihar Kano ne a karan kaina domin jajanta wa Gwamnan Jihar da matarsa, Sarkin Kano da kuma sauran mazauna jihar bisa rasuwar fitaccen malami, Sheikh Ahmad Bamba da Hanifa Abubakar.

“Muna addu’a kuma muna fatan za a yi mata adalci. A matsayina na uwa ina da ’ya’ya da jikoki da ke karatun Firamare yanzu haka, sun yarda da malaman su, mu ma iyaye mun amince da su.

“Don haka idan har yaranmu ba za su ma aminci a makarantunsu ba, hakan na nufin cewa al’umma za ta sauya zuwa wani abu daban.

“Ina gani ya dace a dauki mataki don kare aukuwar makamancin haka a nan gaba.”

Tun a farkon watan Janairu ne Allah Ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci kuma masanin Hadisi, Dokta Ahmad Ibrahim-Bamba rasuwa, inda dubun dubatar mutane ne suka halarci jana’izar a birnin Kano.

A zartar wa wanda ya kashe Hanifa hukuncin kisa a bainar jama’a —Aisha Buhari

Tun bayan bullar rahoton mutuwar Hanifa, Aisha Buhari ta bayyana goyon baya a kan kiraye-kirayen da ake yi na zartar da hukuncin kisa a bainar jama’a ga mutumin nan da ake zargi da kashe dalibar tasa ’yar shekara biyar a Jihar Kano.

A halin yanzu dai an gurfanar da Abdulmalik Tanko a gaban kotu, mammalakin makarantar Noble Kids Academy da ke Unguwar Dakata a Karamar Hukumar Nasarawan Jihar Kano kan kisan dalibar.

Aminiya ta ruwaito yadda tawagar ’yan sanda suka tono gawar Hanifa wadda Abdulmalik Tanko ya binne a makarantar ta Noble Kids bayan kwanaki da sace ta a ranar 4 ga watan Disambar 2021.

A yayin da aka gabatar da shi ga manema labarai, ya ce ya kashe ta ne bayan ya sanya mata shinkafar-bera a cikin shayi sannan ya gididdiba gawarta ya binne a wani rami da ya haka a makarantar.

Wannan batu ya yi matukar tayar da hankalin jama’a inda aka rika yin alla-wadai da tofin Allah tsine a kansa da wadanda suka taimaka masa.

A wani bidiyo da a yanzu ya karade dandalan sada zumunta, wani fitaccen malamin addinin Islama a Kano, Malam Abdallah Gadon Kaya, a daya daga cikin karatuttukansa ya yi kira da a zartar da hukuncin kisa a bainar jama’a kan Abdulmalik Tanko ta irin hanyar da ya kashe dalibar tasa Hanifa.

Malam Abdallah ya yi da’awar cewa, a kashe mutumin a bainar jama’a domin hakan zai zama izina ga kowa, lamarin da ya ce umarni kawai Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano za su bayar kuma aikin gama ya gama.

Ita ma uwargidan shugaban kasar ta wallafa wannan bidiyo na Malam Abdallah a shafinta na Instagram, inda ta bayyana goyon baya dari bisa dari a kan wannan kira.

A sakon da Aisha ta wallafa, ta ce “muna goyon bayan da’awar da Malam ya yi.”