✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tabar wiwi ta sa an tsinka igiyar aure a jihar Oyo

Wata Kotun Al’adu da ke zama a Ibadan ta raba auren wata tela, Adija Adebayo ta mijinta, Ademola Adebayo, saboda shan wiwi da ya ke…

Wata Kotun Al’adu da ke zama a Ibadan ta raba auren wata tela, Adija Adebayo ta mijinta, Ademola Adebayo, saboda shan wiwi da ya ke yi.

Da take bayani a gaban kotun, Adija da ke zaune a unguwar Academy da ke Ibadan, ta ce raba auren ya zama dole saboda dukan dansu mai shekara daya da rabi da Mijin ke yi da kuma lalata mata kayan aiki idan ya sha wiwi.

“Babu abinda ban yi ba don in hana Ademola shan wiwi da ya ke yi amma bai bari ba kuma abun haushin shi ne, ya kan kai dan mu inda suke shan wiwi har yaron ya shaki wiwin ya koyi yadda ake sha.
“A duk lokacin da Ademola ya dawo da yaron gida sai ya rika yin amfani yatsunsa yana kwaikoyon yadda ake shan wiwi kuma har abun ya fara damu na.
“Ademola yana lalata mani kayan dinki, wasu lokutan har keta kayan dinkin mutane yake yi idan muka samu sabani” inji Adija.
Ademola, wanda matukin Bas ne ya ki amince wa da raba auren, inda kuma ya ce maganar shan wiwi da ta yi kazafi ne.
Ya kuma roki kotun a kan kada ta raba auren saboda yana son matarsa da dansa.
“Ina son kotu ta san cewar na yi hakuri da Adija duk da cewa kazama ce, ba ta tsaftace mana gida, kuma tana tarayya da wani malami.
“Mutumin yana kiranta a waya su yi magana da Hausa, suna cin amana ta saboda bana jin Hausa,” inji Ademola.
Bayan sauraron bayanan su, sai Mai shari’a Ademola Odunade, ya raba auren domin a samu zaman lafiya.
Ya kuma ce hakkin kula da tarbiyar yaron yana wuyar matar, inda ya kuma umurci Ademola ya rika biyan ta Naira dubu biyar duk wata a matsayin alawus din abinci da biyan kudin makaranta da sauran dawainiyarsa.