✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tabarbarewar Tsaro: Gombe Ta Kafa Rundunar ‘Operation Hattara’

Gwamnan Gombe Muhammaadu Inuwa Yahaya ya ce duk da jihar na zaune lafiya a yanzu, kaddamar da sabuwar rundunar tsaro ta ‘Operation Hattara’, matakin kariya…

Gwamnan Gombe Muhammaadu Inuwa Yahaya ya ce duk da jihar na zaune lafiya a yanzu, kaddamar da sabuwar rundunar tsaro ta ‘Operation Hattara’, matakin kariya ne daga fadawa matsalar tsaro.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin bude taron zaman lafiya da samar da tsaro mai dorewa da aka gudanar karo na farko a jihar.

Taron wanda ya samu halartar Babban Sufetan ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, da sauran jagorin tsaro, ya duba hanyoyin dakile matsalolin tsaro na zamani da na habaka atttalin arziki da zamnatakewa.

Gwamnan ya bayyana cewa taron zai bayar da dama ga jami’an tsaro, da na gwamnati da ma sauran masu ruwa da tsaki wajen samar da sabbin dabarun tabbatar da dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Yahaya ya ce kafa rundunar tsaron mataki ne na karfafa nasarorin da manufofin gwamnatinsa ta haifar wa jihar da kuma tsara yadda za a magance tashe-tashen hankula a tsakanin matasa, kasancewar jihar na fuskantar tashe-tsahen hankula na cikin gida.

Ya ce baya ga rashin aikin yi da ya haifar da hakan, akwai dabar siyasa da ke ruruta wutar tashin hankalin da matasan ke yi.

Wannan ne a cewarsa ya sanya aka dauki matasa 500 a matsayin jami’an tsaro da zirga-zirga da muhalli na jihar Gombe (GOSTEC), da zummar tallafa wa hukumomin jihar wajen tabbatar da doka da oda.

A nasa bangaren Babban Sufeton ’Yan Sandan, ya yi alkawarin bayar da goyon bayansa da kuma zurfafa hadin guiwa da al’umma wajen dakile miyagun laifuka a fadin Najeriya.